BBC ta karrama matan da suka lashe gasar Hikayata ta 2017

Hikayata
Bayanan hoto, Maimuna Idris Sani Beli wadda ta lashe gasar a shekarar 2017

Gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai na shekarar 2017.

An gudanar da bikin karrawar ne a otel din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ranar Juma'a.

Maimuna Idris Sani Beli ta zama gwarzuwar gasar a bana, inda aka ba ta lambar yabo da kuma $2000.

Maimuna, wacce ta fito daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labarinta ne mai suna "Bai Kai Zuci Ba".

"Fasalin bayar da labarin", a cewar jagoran alkalan, Farfesa Ibrahim Malumfashi, "da yadda ya ginu, da yadda aka fita daga duniyar da muke ciki aka koma lahira; daga lahirar aka dawo Najeriya, a cikin Najeriyar kuma aka bi wurare daban-daban aka gina labarin."

Hikayata
Bayanan hoto, Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu

Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu, da labarinta mai suna "Zawarcina", yayin da Habiba Abubakar da Hindatu Sama'ila Nabame Argungu ne suka yi na uku a labarin hadin gwiwa da suka shigar, mai suna "Sana'a Sa'a".

An zabi labaran ne bayan fafatawar da matan da suka shiga gasar suka yi, kana alkalai kan gasar suka tantance labarai uku da suka dace da ka'idojin da aka shimfida.

Hikayata
Bayanan hoto, Habiba Abubakar da kuma Hindatu Sama'ila Nabame Argungu (daga dama) wadanda suka yi na uku

Da take karbar lambar yabonta, Maimuna ta yi godiya ga Sashen Hausa na BBC bisa wannan gasa da ya kirkiro ta mata zalla.

Wannan ne karo na biyu da BBC ta sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla.

Editan Sashen Hausa na BBC, Jimeh Saleh, ya ce: "Ko shakka babu kwalliya ta biya kudin sabulu da ma makasudin fito da gasar shi ne a karfafawa iyayenmu mata gwiwa don bunkasa basirar da Allah Ya yi musu ta fannin adabin Hausa."

Ya ci gaba da cewa "kuma hakan mun ga ci gaba kwarai da gaske. Mun tashi daga labarai 300 a bara zuwa fiye da labarai 400 a bana."

Shugaban ya ce ana aikin yin wani kundi wanda za a wallafa kuma zai kunshi labarai da suka yi zarra a bara da kuma bana.

Bayanan bidiyo, Bayanin alkalin gasar Hikayata kan labaran da suka yi nasara

Karanta wadansu karin labarai