An kashe mutum 235 a masallacin Juma'a a Masar

The militants targeted a mosque near al-Arish

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kai harin ne a wani masallaci kusa da garin al-Arish

An kai wani harin bam a wani masallacin Juma'a da ke yankin arewacin Sinai na kasar Masar, inda ya kashe akalla mutane 235, kamar yadda kafar yada labarai ta kasar ta bayyana.

Wadansu ganau sun ce an kai harin ne a masallacin al-Rawda wanda yake garin Bir al-Arish yayin da ake sallar Juma'a.

'Yan sanda sun ce wadansu mutane hudu ne da ke kan wani abin hawa suka bude wa masallatan wuta.

Kasar Masar tana fama da rikice-rikice masu nasaba da 'yan gwagwarmaya a yankin Sinai tun a shekarar 2013.

An sha fuskantar hare-hare 'yan gwagwarmaya a yankin Sinai, amma wannan ne hari mafi muni a yankin.

Wadansu hotuna da suka fito daga masallacin sun nuna mutanen da abin da ya rutsa da su cikin jini.

Akwai akalla mutane 125 da suka ji raunuka, a cewar wani rahoto.

map

Wani rahoto ya ce an nufi harin ne a kan wadansu mutane da suke goyon bayan jami'an tsaron kasar wadanda suke salla a masallacin.

Wadansu mutane sun ce mabiya darikar Sufaye suna yawan halartar masallacin Juma'ar.

Kungiyoyin 'yan gwagwarya ciki har da kungiyar IS suna ganin Sufaye a matsayin wadanda akidarsu ta sha bamban da sauran Musulmi.

Sai dai har yanzu babu wadda ya dauki alhakin harin.

Karanta wadansu karin labarai