An kai wadda ake zargi da kashe mijinta gidan yari a Abuja

    • Marubuci, Abdulwasiu Hassan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Matar da ake zargi da kashe mijinta, Maryam Sanda, ta bayyana a gaban wata babbar kotu da ke Abuja ranar Juma'a.

Ana zargin ta ne da kashe mai gidanta, Bilyaminu Bello, bayan ta daba masa kwalba a sassan jikinsa.

Al'amarin ya faru ne a gidan ma'auratan da ke unguwar Wuse a Abuja.

Lauya mai shigar da kara ya ce suna so su sauya tuhume-tuhume saboda sabbin hujjoji da aka samu sakamakon bincken da ake yi mata.

Maryam ta shiga kotun ne tana rungume da jaririyarta da kuma Al-Kur'ani a hannunta, inda ta lullube fuskarta ba a iya gani.

An karanta mata tuhume-tuhume da ake mata.

Ana tuhumurta da daba wa mijinta fasasshiyar kwalba a kirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa, amma ta musanta hakan tana mai zubar da hawaye.

Tuhuma ta biyu an ce ta ji masa ciwo da kwalba a kirji wanda ya yi sanadin mutuwarsa, a nan ma Maryam ba ta amsa yin laifin ba.

Lauya mai kare wadda ake kara ya ce ba sa sukar dage zaman shari'ar sai dai suna so a ba da wadda ake zargi beli.

Kotun dai ta bayar da umarni a atsare ta a gidan yari na Suleja.

Daga nan ne Alkalin Kotun Yusuf Halilu ya dage zaman shari'ar zuwa ranar 7 ga watan Disamba.