Killace shanunmu zai yi wuya a Benue - Makiyaya

Benue anti-Grazing Law
Bayanan hoto, Makiyaya na ci gaba da kora shanunsu a titunan birnin Makurdi duk da dokar hana yawo da dabbobi ta jihar Binuwai

Da alama dokar hana kiwon sake da gwamnatin jihar Benue a tsakiyar Najeriya ta kafa ta gamu da cikas wajen aiki da ita, domin kuwa masu kiwon sake a jihar na ci gaba da cin karansu ba babbaka.

A yayin da tawagar BBC ta shiga birnin Makurdi ta yi kicibis da wani makiyayi da ya ke kora shanunsa mashaya, wanda ya ce ba za su iya killace dabbobinsu ba ruwa ba.

Haka kuma da yammacin ranar Talata ma wakilan BBC sun gamu da wani makiyayin a cikin wata unguwa a tsakiyar birnin Makurdi yana mayar da shanunsa gida, bayan sun yini a makiyaya.

To sai dai duk da haka hukumomin jihar suna cewa dokar ta fara aiki, kuma ma a wasu wuraren hukumomin sun kama dabbobin da ke kiwon sake da dama, da suka hada da shanu, da awaki, da tumaki, da kuma aladai.

Gwamnatin Jihar Binuwai dai ta kafa dokar hana kiwon sake a jihar domin magance rikece-rikcen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma.

Dokar ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Nuwambar 2017, to sai dai fulani makiyaya na cewa dokar ta yi musu mugun tanadi, to amma gwamnatin jihar ta ce ta yi dokar ne domin maslahar kowa.

Benue anti-Grazing Law
Bayanan hoto, Wani makiyayi da BBC ta zanta da shi a Makurdi ya ce su ma ba su ci sun koshi ba, ballantana su yi ciyar da dabbobinsu a killace
Benue anti-Grazing Law
Bayanan hoto, Makiyaya a birnin Makurdi na cewa sun fita kiwo da shanunsu ne saboda sun ji cewar kungiyoyinsu sun shigar da kara kan dokar haramta kiwon sake a gaban kotu