Kasafin da Buhari ya gabatar 'bukata ce kawai'

Mai tsawatarwa a Majalisar Wakilan Najeriya, Honourable Alhassan Ado Doguwa ya ce a tsarin aiki duk duniya babu kalmar cushe a aikin 'yan majalisa, sai dai fa idan abin ya fito daga bangaren zartarwa.
Ya ce bangaren majalisa ne tsarin mulki ya ba wa ikon yin aiki kai tsaye a kan abin da shugaban kasa ya gabatar.
"Kalmar cushe ta samo asali ne idan a bangaren gwamnati wata hukuma ko ma'aikata ko minista ko wani jami'i ya shigo da wani abu (cikin kudurin kasafin kudi) ba tare da amincewar shugaban kasa ba" in ji shi.
Ranar Talata ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin kudin 2018 wanda ya kai naira Tiriliyan 8.6 a gaban hadin gwiwar majalisun dokokin kasar.
A baya dai an sha fama da ce-ce-ku-ce game da zargin yin cushe a kasafin kudi, lamarin da kan haddasa jinkiri wajen amincewa da kuma zartar da shi zuwa doka tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa.
Alhassan Doguwa ya ce daga lokacin da shugaban kasa ya ajiye kudurin kasafin kudi a gaban majalisa, "daidai yake da shafa labari shuni. Daidai yake da bukata kawai, ba doka ba ce".
A cewar dan majalisar abin da su suka yi aiki a kansa, suka cire, suka rage, suka kara ko suka daidaita shi ne abin da shugaban kasa zai yi aiki da shi.
Shugaban Najeriya ya gabatar da kudurin kasafin kudin 2018 ne a wannan karo da wuri sabanin yadda abin yake shekarun baya, don samun amincewar majalisun kasar a kan lokaci.
Sai dai Alhassan Doguwa ya ce abu ne mai wahala majalisun su iya kammala aikin kafin shiga sabuwar shekara.
"Amma dai ina so in tabbatar maka cewa kowannenmu ya daura aniya don a biya wa shugaban kasa wannan bukata don yi wa kasar nan kyakkyawan tsari ta fuskar tattalin arziki." In ji Doguwa.
Ya yaba wa Shugaba Buhari kan yadda ya yi kokarin gabatar da kasafin kudin a kan lokaci, wanda "a baya ba taba yin haka ba a tarihin siyasar Najeriya".
Mai tsawatarwar ya ba da tabbacin cewa su ma a nasu bangare za su yi kokarin kammala aikinsu da wuri fiye da a kowanne lokaci a baya.











