China: Jam'iyyar kwaminis za ta zabi sabbin shugabanni

China ta fara gudanar da taron siyasa mafi girma da muhimmanci a Beijing babban birnin kasar.

Ana sa ran cewa fiye da wakilai 2,000 ne zasu hallara, inda kuma aka inganta tsaro a babban birnin.

Ana gudanar da wannan taron a kowace shekara biyar, kuma a lokacin taron ne ake zaban wadanda suke jagorantar kasar da kuma alkiblar da zata dauka cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shugaba Xi Jinping ya zama shugaban China a shekarar 2012, kuma ana kyautata zaton zai cigaba da rike mukaminsa na babban jagoran jam'iyyar kwamunisanci mai mulkin kasar. Ya gabatar da jawabin bude wannan taron ne a gaban wakilai kimanin 2,000 daga dukkan sassa na kasar.

Shugaba Xi ya fara jawabinsa ne da bayyana jadawalin cigaban da kasar China ta samu tun da ya zama shugaban kasa, kuma ya ce "tsarin kwamunisanci irin salon na China ya shiga wani sabon karni".

Ya kuma yi kira ga 'yan jam'iyyar tasu da su "cigaba da kokarin samar da rayuwa mai inganci ga al'umomin kasar".

A lokacin wannan babban taron ne za a zabi sabbin jami'an kwamitin koli dake gudanar da kasar, wato Politburo, kana a fitar da abon jadawalin alkiblar kasar na shekara biyar masu zuwa.

Ana sa ran a kammala babban taron a cikin mako mai zuwa.

An kayata birnin na Beijing da furanni da sauran kaya masu kawatawa domin wannan bababn taron.

Amma an inganta tsaro a dukkan sassa na birnin. A farkon makon nan, an rika ganin dogayen layuka a tasoshin jiragen kasa domin binciken da jami'an tsaro kan yi ga matafiya.

Taron kolin kuma ya janyo cikas ga cibiyoyin kasuwanci, inda aka rufe wasu gidajen abinci da na motsa jiki da kulob-kulob din shakatawa domin karuwar matakan bincike.

Domin shirin tsuke baki da shugaba Xi Jinping yake aiwatarwa, da alama wakilai a wajen taron na yau zasu fuskanci raguwar kayan more rayuwa, inda wasu rahotanni daga China ke cewa otel-otel a birnin zasu rage yawan kayan alatun da za a yi amfani da su.

Yawancin masu lura da al'amuran da ke kai-kawo a kasar sun tabbatar cewa shugaba Xi zai yi amfani da damar da wannan taron zai ba shi domin ya fadada ikonsa a kan jam'iyyar.

Ana sa ran jam'iyyar ta sake rubuta tsarin mulkin da ake gudanar da ita domin a sanya shirinsa a ciki - wanda zai daukaka martabar shugaba Xi ta kai na tsofaffin shugabannin da suka gabata kamar Mao Zedong da Deng Xiaoping.

Tun bayan da ya dare karagar mulkin kasar, shugaba Xi ya kara karfin ikonsa a jam'iyyar, kuma ya rika daukan matakan rage cin hanci da rashawa a cikin jam'iyyar da ma sauran sassan na rayuwa, inda aka rika sa ido akan tace dukkan abubuwan da ake wallafawa, kana an rika kama lauyoyi da masu rajin kare hakkokin jama'a

A karkashin shugab Xi, an habaka shirin China na zamanantarwa da jaddada cigaban kasar inda China ke nuna matsayinta da muhimmancinta a tsakanin kasashen duniya.

Babu shakka shugaba Xi na da goyon bayan ilahirin jama'ar kasar China.