Ivory Coast: Mutum hudu sun mutu a hadarin jirgin sama

Asalin hoton, Reuters
Wani jirgin saman kaya ya yi hadari a kusa da gabar tekun kasar Ivory Coast jim kadan bayan ya tashi daga filin jirgin saman birnin Abidjan.
Rahotanni sun ce mutane da dama ne suka rasa rayukansu.
Hadarin ya faru ne lokacin da ake maka ruwan sama karmar da bakin kwarya.
Jirgin yana dauke ne da wadansu kayayyakin sojin kasar Faransa, kamar yadda wata kafar yada labarai ta bayyana.

Asalin hoton, Reuters
Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa akalla mutum hudu ne suka mutu.
Masu aikin ceto sun fito da gawawwaki guda biyu daga cikin jirgin, akwai kuma sauran biyun a cikin buraguzan jirgin, kamar yadda kamfanin Reuters ya ruwaito.
Sai dai wadansu rahotanni sun ce galibin ma'aikatan jirgin sun tsira.







