Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An samu rigakafin 'cutar Ebola'
Sakamakon farko na gwajin alluran rigakafin cutar Ebola har iri biyu, ya nuna cewa duka biyun na iya kare mutane daga daukar cutar tsawon akalla shekara guda.
An gudanar da binciken ne a kasar Liberia inda aka gwada rigakafin kan marasa lafiya dubu daya da dari biyar.
Wadanda aka yi wa rigakafin sun samu kariya daga daukar cutar tsawon shekara guda.
Gwajin ya nuna cewa ana iya amfani da rigakafin wurin ceto rayukan al'umma duk lokacin da annobar Ebola ta sake barkewa nan gaba.
Cutar Ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrika a shekarar 2014.