Guguwa ta yi kaca-kaca da manyan jiragen ruwa da gidan rainon yara

Wata mahaukaciyar guguwa ta yi kaca-kaca da manyan jiragen ruwan daukar kaya, kuma a kalla mutum takwas ne suka mutu sakamakon ruwan sama da aka sheka kamar da bakin kwarya a yankin KwaZulu-Natal na Afrika Ta Kudu.

Daga cikin wadanda suku mutu har da wani yaro da ruwa ya tafi da shi, kuma wadansu marasa lafiya sun rasa ransu bayan da wani gini ya fado musu a asibitin Prince Mshiyeni Memorial, kusa da birnin Durban, babban birnin yankin.

Hukumar Kula da Yanayi ta Afrika Ta Kudu ta ce, ''Ruwa mai matukar karfi ya yi barna a KwaZulu-Natal da wasu sassan kasar'' .

Irin wannan ruwa dai kan zo ne tare da iska mai karfi da kuma mahaukaciyar guguwa.

Kafar yada labarai ta TimesLive ta ambato mai magana da yawun Hukumar Kula da Yanayi Hannelee Doubel, yana cewa: ''Hotunan da aka dauka daga tauraron dan adam sun nuna yadda aka dinga walkiya a saman teku, har zuwa gabar tekun,''

''Ruwan ya tilasta rufe tashar jiragen ruwa ta Durban, daya daga cikin wadanda aka fi amfani da su a Afrika, a ranar Talata.

Jirage guda uku sun kafe a yayin da wadansu suka tsunke daga igiyoyin da ke rike da su kuma ruwa ya yi awon gaba da su, a cewar hukumar tashar jiragen ruwan.

Wani ma'aikacin agajin gaggawa, Paul Herbst, ya ce ambaliyar ruwa ta tafi da wata karamar yarinya a Umlazi, a unguwa da ke Kudancin Durban.

Ya ce: ''Wani wajen rainon yara da ke kusa da wani kogi ya yi ambaliya.''

Malamar da ke aiki a wajen ta yi kokarin rike yara uku amma sai dai yaro na hudun ya kufce ruwa ya tafi da shi.