Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama wadanda suka 'jibgi' dan Nigeria a India
'Yan sanda a Delhi babban birnin Indiya sun ce sun kama mutum biyar wadanda ake zargi da yi wa wani dan Najeriya dukan kawo wuka.
A ranar Talata ne kafofin watsa labarai a Indiya suka nuna bidiyon da ke nuna yadda wasu gungun Indiyawa suka lakadawa wani dan Najeriya duka a birnin Delhi.
'Yan sanda sun kuma tsare mutumin Najeriyar wanda ayarin wasu magidanta a Delhi suka zarga da sata.
A cikin bidiyon, an ga mutane guda hudu ko biyar na amfani da sanduna suna rafka wa mutumin, bayan an daure shi a jikin wani turke.
Ko lokacin da yake roko Allah-Annabi a yi masa afuwa wani mutum ya kama kafafuwansa, inda wani ya rika zane shi a tafukansa.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun afkuwar irin wannan lamari ba a Indiya, ko a watan Afrilun da ya gabata ma an kai wa wasu dalibai 'yan Najeriya hari a Delhi, inda aka musu duka.
A wancan lokacin har sai da jakadun ƙasashen Afirka a Delhi suka yi Allah wadai da hare-haren da aka kai din.
Kazalika an sha kai wa 'yan wasu kasashen Afirka da dama hari a sassa daban-daban na Indiya.