India: An lakadawa dan Nigeria dukan kawo wuka

Kafofin watsa labarai a Indiya sun nuna wani bidiyo dake nuna yadda wasu gungun Indiyawa suka lakadawa wani dan Najeriya duka a birnin Delhi.

Kamfanin dillancin labarai na ANI ya ce an nadi bidiyon ne ranar 24 ga watan Satumba.

Ana iya ganin yadda Indiyawan suka rika dukan mutumin da sanduna a cikin bidiyon, bayan da suka daure masa kafafunsa da wani turken lantarki:

Tashar talabijin ta NDTV dake Indiya ta bada rahoton cewa mazauna unguwar ne suka tuhumi mutumin da yin sata a cikin wani gida.

Daga baya sun mika dan Najeriyan ga jami'an 'yan sanda bayan wannan harin, kuma an ga rauni a kansa da fuskarsa da kafafunsa har ma da bayansa, inji rahotan.

'Yan sanda sun sanar da tashar NDTV cewa sun gurfanar da dan Najeriyan a gaban wani alkali bayan da aka duba lafiyarsa a asibiti, kuma alkalin ya bada umarnin a tsare shi a kurkuku.

Amma 'yan sandan sun ce zasu dauki mataki a kan wadanda suka ci zarafinsa sabili da hotunan bidiyon da suke bincike a kai, inji tashar talabijin din.