Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Annobar kyandar biri ta barke a jihar Bayelsa da ke Nigeria
An samu barkewar annobar kyandar biri a jihar Bayelsa da ke Kudu maso kudancin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Kwamishinan lafiya na jihar Ebitimitula Etebu, ya tabbatar wa da BBC cewa tuni aka kebe mutum 10 da suka kamu da cutar, ana kuma neman wasu da ake tunanin sun kamu don su ma a kebe su.
Sai dai kwamishinan bai tabbatar da wasu rahotannin da ke cewa mutum 10 sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ba.
Mista Etebu, ya ce tuni aka aike da samfurin kwayoyin cutar dakin gwaje-gwaje na Hukumar Lafiya Ta Duniya da ke Senegal don tantancewa, kuma sakamakon gwajin ne zai tabbatar ko annoba ce.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, daga cikin mutum 10 da aka kebe akwai wani likita, kuma a kalla mutum 49 ake nema don a kebe su wadanda ake zaton sun kamu da cutar
Cutar ta samo asali ne daga jikin biri da saura dabbobin da ke shiga jeji kamar su bera da kurege da barewa.