Kalli hotunan ziyarar da Buhari ya kai Maiduguri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara garin Maiduguri na jihar Borno a karon farko tun bayan hawansa mulki a watan Mayun shekarar 2015.

Ya kai ziyarar ne a ranar da kasar take bikin cika shekara 57 da samun 'yancin kai.

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ne ya tarbi Shugaba Buhari lokacin da ya isa jihar jim kadan bayan ya yi wa al'ummar kasar jawabi ranar Lahadi da safe.

Shugaban ya kai ziyara ne babban barikin sojin kasar wato na rundunar Operation Lafiya Dole da ke Maiduguri.

Shugaban ya yi wa sojojin jawabi, inda ya yaba da gudunmuwa da kuma yadda suke sadaukar da kansu wajen kare kasar.

Hakazalika ya bukaci sojojin da su kara kaimi, inda ya ba su tabbacin ci gaba da ba su dukkannin goyon bayan da suke bukata.

Jihar Borno wadda take yankin arewa-maso-gabashin kasar, nan ne wurin da rikicin Boko Haram ya fi kamari.

Daga babban barikin sojin, shugaban bai zarce ko ina ba, ya koma Abuja.