Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda wani ango ya bata kwalliyar angwancinsa wajen ceto yaro
Yayin da ake cikin daukar hoton liyafar wani aure a kasar Canada, kawai sai lamarin ya dauki wani sabon salo a lokacin da angon ya yi tsalle cikin wani rafi don ceto wani yaro da ya nutse cikin ruwan.
Clayton da Brittany Cook suna jeru don daukar hoto a kan gadar wani wajen shakatawa a birnin Cambridge na jihar Ontario, lokacin da Angon ya lura da wani yaro a firgice a cikin rafi.
Bai yi tunanin kayansa na angwanci ba, sai kawai Mista Cook ya yi tsalle cikin ruwan ya ceto yaro zuwa inda ya fito da shi bakin rafin.
Mai daukar hoton ne ya dauki hotunan yadda aka ceto yaron.
Hotunan sun yadu kamar wutar daji.
Clayton fa fadawa BBC cewa: ''Yaran suna ta bin mu na tsawon mintoci, ni kuwa ina ta lura da su saboda suna tsaye kusa da rafin.''
''A lokacin da Brittany take daukar hoto ita kadai sai na gano cewa yaran guda biyu na tsaye a bakin duwatsu.
''Sai na ga wani yaro a cikin ruwan yana kokarin dago kansa, a lokacin ne na yi tsalle na afka cikin rafin.
''Kawai sai na tsamo shi daga cikin ruwan, kuma ba abin da ya same shi.''
Matar Clayton ta ce da farko ta zaci wasa yake yi da ya yi tsalle cikin ruwan.
Ta ce: ''Ina ganin mutane da dama ma, irin wannan matakin za su dauka.''
''Juyawar da zan yi, sai na ga har ya fiddo da yaron bakin rafin,'' in ji mai daukar hoto Darren Hatt a hirarsa da BBC.
''Don haka na ci gaba da aikina na daukar labaran ranar na hada har da wannan.''
Bayan an ceto shi, babu alamar da ke nuna cewa yaron ya yi rauni amma sai dai ya nuna alamar tsorata, sai ya tafi da yayansa.
Misis Cook ta ce tunanin da mijinta yake yi cikin hanzari da kuma kaunar jama'a da yake yi shi ya sa ta fara son shi da farko.
''Clayton nawa kenan abin sona, wannan kadan kenan daga cikin bajintarsa nan da nan ba bata lokaci," a hirarta da kafar yada labarai ta CTV.