Benzema ya tsawaita zamansa a Madrid

Dan wasan gaban Real Madrid, Karim Benzema, ya tsawaita zamansa a kungiyar na shekara hudu.

Dan wasan mai shekara 29 ya ci kwallo 181 a wasa 371 da ya buga wa Madrid, tun komawarsa can da taka-leda daga kulob din Lyon a shekarar 2009.

Shi ne dan wasa na hudu na kulob din Madrid da ya sabunta yarjejeniyarsa, bayan mai tsaron baya Dani Carvajal da Marcelo da kuma mai Isco.

Benzema ya lashe kofi 14 a Madrid, ciki har da na Zakarun Turai uku da na La Liga biyu.