Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wake da shinkafa sun cika gwamnatin Buhari – Rafsanjani
Tun bayan komawar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari gida, bayan shafe watanni yana jinya a birnin Landan, daya daga cikin abin da aka zuba ido akai shi ne yi wa gwamnatinsa garanbawul, domin fitar da wasu da ake yi wa kallon sun zame wa gwamnatin karfen-kafa.
Malam Auwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar CISLAC, mai sa ido kan ayyukan majalisar dokoki a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa lallai akwai bukatar Shugaba Buhari yayi awon-gaba da wasu da ke ja wa gwamnatinsa bakin jini.
Ka latsa alamar lasifika don jin cikakkiyar hirar da Rafsanjani ya yi da Ahmad Abba Abdullahi: