Babba-da-jaka ya mamaye Australia

Masu filaye da kwararru kan muhalli a kasar Australia suna gargadin cewa yawan babba-da-jaka na neman zama yadda kasar ba za ta iya dauka ba, saboda haka suka bukaci jama'a su rika cin naman dabbar dawan.

Alkaluman gwamnati sun nuna cewa yawan babba-da-jaka a shekara ta 2016 ya kai kusan miliyan 45, wanda kusan ya linka yawan jama'ara kasar biyu.

A shekara ta 2010 yawansu miliyan 27 ne kawai, inda aka danganta karuwar tasu a kan yawan ruwan sama da ya samar da tarin abincin ga dabbar.

Sai dai yawancin masana na fargabar cewa miliyoyin dabbar za su kamu da yunwa idan aka aka samu bazarar da ba ruwan sama.

Kasar Australia tana da tsauraran dokoki a kan kashe dabbar, inda kowace jiha take da iyakar lasisin da take bayarwa na farautar dabbatr ta yadda za a bar iya yawan da jihar za ta iya dauka.

Kafafen watsa labarai na kasar sun ce, mutane ba su karbi yawancin lasisin farautar dabbar ba, saboda naman dabbar ba shi da kasuwa sosai yanzu.

A duk shekara ana samun takaddama a kan kashe dabbar, inda masu rajin kare hakkin dabbar ke cewa babu wata sheda da ke nuna cewa rage yawanta zai taimaka wa muhalli.

Za a iya amfani da fatar dabbar, wajen siyarwa a kai kasashen waje, amma kuma yawanci ana asarar namanta ne saboda ba kasafai ake samun masu bukatarsa ba, kamar yadda bayanan shafin intanet na hukumar kula da muhalli ta Australia ya nuna.

Saboda babba-da-jaka dabba ce da ke da matsayi a Australia, ana kyamar cin namanta sosai.