Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
India: Kotu ta yarda a zubar da cikin 'yar shekara 13 da aka yi wa fyade
Kotun kolin Indiya ta bayar da izinin zubar da cikin wata yarinya 'yar shekara 13 da aka yi wa fyade a birnin Mumbai na kasar.
Yarinyar, wadda ke dauke da cikin mako 32, ta nemi kotu ta bayar da damar yin hakan tun da dokar Indiya ta yarda da zubar da cikin da ya kai mako 20 ne kawai idan har rayuwar mai cikin na cikin hadari.
Lauyan yarinyar ya shaida wa BBC cewa a ranar Juma'a ne za a zubar da cikin.
An gano yarinyar tana da ciki ne lokacin da iyayenta suka kai ta asibiti domin a shawo kan muguwar tebar da suka fahimci tana yi.
Yarinyar dai ta ce abokin aikin mahaifinta ne ya yi mata fyade. Tuni aka kama shi.
Wasu alkalai uku ne suka yanke hukunci bayar da umarnin zubar da cikin, bayan da babban alkalin daga cikin su Dipak Mishra, ya ga rahoton asibitin da wata tawagar likitoci daga asibitin JJ da ke Mumbai suka rubuta.
Rahoton ya ce yarinyar mai shekara 13 za ta fuskanci hadari idan an zubar da cikin a yanzu ko idan aka jinkirta zuwa nan gaba.
Likitocin sun bayar da shawarar a jinkirta zubar da cikin zuwa nan da mako biyu don dan tayin ya sake girma, amma alkalan suka bayar da umarnin gaggawar zubar da shi don gudun kada yarinyar ta shiga cikin tashin hankali.
Dr Nikhil Datar, wanda shi ne likitan da ya gano yarinyar na da ciki a ranar 9 ga watan Agusta, lokacin da iyayenta suka kai ta asibiti a tunanin kiba ta yi mata yawa, ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a ranar Laraba da cewa, ba a taba yin irinsa ba.
Wannan al'amari na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wata yarinya 'yar shekara 10 ta haihu, sakamakon fyade da Kawunta ya yi mata a birnin Chandigarh.
Ita ma cikinta ya kai mako 32 amma kotu ta hana a zubar mata da cikin bayan da likitoci suka ce hakan na da matukar hadari ga rayuwarta.
A watan Mayu ma, an samu irin wannan al'amari a jihar Haryana, inda aka hana zubar da cikin wata 'yar shekara 10 din da mijin mahaifiyarta ya yi wa fyade.
Wakiliyar BBC a birnin Delhi Geeta Pandey, ta ce irin wadannan al'amura da ke faruwa a baya-bayan nan na girgiza al'ummar Indiya, inda ake ta kiraye-kirayen daukar matakan dakile hakan.
"Abin yana munana ne saboda yaran kansu ba sa gane halin da suke ciki, kuma iyayensu ba sa taba kawo cewa 'ya'yansu za su yi ciki a kananan shekarunsu," in ji Geeta.
Kololuwar cin zarafin yara a Indiya
- Duk cikin kasa da sa'a uku a kan yi wa yarinya daya 'yar shekara 16 fyade, yayin da ake yi wa 'yar shekara 10 fyade duk cikin sa'a 13
- An yi wa yara fiye da 10,000 fyade a shekarar 2015
- Ana yi wa mata miliyan 240 da ke zaune a Indiya aure kafin su cika shekera 18
- Kashi 53.22% na yara da ke karatu a makarantun gwamnati sun bayar da rahoton cewa ana yin lalata da su
- Kashi 50% na masu aikata wannan mummunan abu wadanda suka san yaran ne ko ma 'yan uwansu na jiki
Bayanai: Gwamnatin Indiya da Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya Unicef