Beraye sun haddasa ambaliyar ruwa a India – Minista

Wani minista a jihar Bihar ta India ya dora alhakin ambaliyar da ta auku a kwanan nan wadda ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 500, da tilasta wa wasu sama da miliyan 12 tserewa daga gidajensu a kan beraye.

Ministan albarkatun ruwa, Rajiv Ranjan, ya ce beraye ne suka yi hudoji a jikin bangon jingar da aka yi wadda ta kare ruwan, abin da ya sa jingar ta yi rauni har ruwan ya ratsa ta cikinta.

Mista Ranjan ya ce kayan abincin da kauyawan wurin ke adanawa a kusa da jingar da aka yi don kare ruwan kogin da ke wurin, su suka jawo berayen suka huhhuda bangon jingar har ruwa ya balle ta wurin.

'Yan hamayya sun soki ministan a kan kalaman nasa, da cewa kawai dai gwamnati ba ta shirya tunkarar matsalar ta ambaliya wadda ake fama da ita a kowace shekara ba.

Kwararru sun ce mamakon ruwan saman da aka samu a bana shi ya haddasa ambaliyar wadda ta fi muni a gomman shekaru a kasar ta India.

Masu rajin kare hakkin dan adam sun soki gwamnati da gina tituna da sauran abubuwa ba tare da la'akari da bukatar yin magudanun ruwa yadda ya kamata ba.

A farkon wannan shekara wani rahoto da gwamnati ta fitar ya ce a yawancin jihohin kasar ta India, ba a bayyana yankunan da ake ganin suna cikin hadarin ambaliya ba, ta yadda za a iya shirya mata kafin ta auku.