Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An hukunta marubuci saboda kamanta Sarkin Saudiyya da Allah
An dakatar da wani marubuci a kasar Saudiyya bayan da ya wuce gona da iri wajen kambama Sarkin kasar Salman.
Marubucin, Ramadan al-Anzi ya yabawa sarkin a cikin jaridar al-Jazirah ta hanyar amfani da sunayen da na Allah ne.
Duk da yake yawanta yabo abu ne da a ka saba da shi - ba a son hada wani sarki da Ubangiji.
Saboda haka Sarki Salman, wanda ya "kadu matuka," ya aika da umarnin cewa a dakatar da Mista Anzi, in ji rahotanni daga kafafen watsa labarai.
Jaridar ta riga ta wallafa sakon ban hakuri a ranar Jumma'a, inda Mista Anzi ya yaba wa Sarkin da sunaye kamar "Haleem" da "Shadeed al-Eqab", wadanda sunaye ne na Allah.
Wasu kafafen watsa labarai a Saudiyya sun yi kira da a dauki karin matakai domin hukunta jaridar.