Abba Kyari: 'Evans ya so ya gagari jami'an tsaron Nigeria'

Mataimakin Kwamishinan dan-sandan da ya jagoranci cafke madugun da ake zargi da garkuwa da jama'a da dama domin neman kudin fansa a Najeriya, ACP Abba Kyari, ya shaida wa BBC irin jan aikin da suka yi wajen cafke madugun.
A farkon wannan watan ne jami'an 'yan sanda a Legas suka yi nasarar kama Mista Chukwudi Onuwamadike wanda aka fi sani da sunan Evans bayan sun kwashe shekara bakwai suna farautarsa.
"Ya gagari dukannin jami'an tsaron Najeriya a tsawon kusan kimanin shekara bakwai," in ji Abba Kyari a wata hira da BBC.
Har ila yau, Kyari ya ce Evans ya kwashe fiye da shekara 20 yana aikata laifuka a kasar.
"Ya kware sosai. Yana da layukan waya fiye da guda 100," in ji Kyari.
Sai dai har yanzu ba a gurfanar da Evans gaban kuliya ba domin jin ko zai amsa ko musanta laifukan da ake tuhumarsa.












