Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kamaru: Tsananin zafi yasa mutane rufin jinka
Sakamakon tsananin zafin da ake yi a yankin arewacin Kamaru ya sa mutane sun rungumi hanyar rufin daki da ciyawa.
Matsalar ta kara kamari ne saboda karancin wutar lantarki da zai ba wa jama'a damar sanyaya dakuna da na'urori na zamani.
Hakan ya sa wasu suka koma wa rufin dakuna da jinka wadda ake yi da busasshiyar ciyawa.
Yin amfani da jinkar na bai wa jama'a samun kariya daga zafin rana da kuma kura.
Wani wanda ke sakar jinkar, Nura Isyaku ya ce rufin na daukar shekaru kimanin biyar kafin ka sake jinkar.
Inda ya kara da cewa rufin jinkar kan hana jin karar zubar ruwan sama a kan rufin kwano.
Wani magidanci ya bayyana cewa rufin jinkar na taimaka wa mutane su samu bacci da daddare saboda zafi ba zai dame su ba.