Nigeria: Shugaba Buhari ya kusa dawowa, in ji matarsa Aisha

Uwargidan Shugaban Najeriya Hajiya Aisha Buhari ta ce mijinta na murmurewa sosai kuma nan gaba kadan zai komo gida daga jinyar da yake yi a kasar Ingila.

Tana magana ne a safiyar Talata bayan da ta dawo daga London, inda ta kai masa ziyarar mako guda.

Wata guda kenan da shugaba Muhammadu Buhari, mai shekara 74, ya bar kasar zuwa Birtaniya - wacce ita ce tafiyarsa jinya karo na biyu a bana.

Hajiya Aisha ta ce shugaban ya "godewa 'yan kasar kan addu'o'in da suke yi masa da kuma goyon bayan da suke bai wa Mukaddashinsa Yemi Osinbajo".

Sai dai rashin lafiyar shugaban tana janyo ce-ce-ku-ce sosai a kasar, inda wasu ke ganin kamata ya yi shugaban ya yi murabus ya fuskanci kula da lafiyarsa.

Amma wasu kuwa suna ganin tun da ya mika ragamar shugabanci a hannun mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, to babu wani abin damuwa.

Har yanzu dai ba a san takamaimai cutar da ke damun Shugaba Buhari ba.

Rashin lafiya ta mamaye rayuwar Buhari a 2017

  • 19 ga watan Janairu ya tafi Birtania hutun jinya
  • 5 ga watan Fabreru ya nemi majilisa da ta tsawaita hutun nasa
  • 10 ga watan Maris ya dawo gida to sai dai bai koma aiki ba kai tsaya
  • 26 ga watan Afrilu ya kasa halartar taron majalasar zartarwa karo na biyu, inda ya rinka "aiki daga gida"
  • 28 ga watan Afurilu bai halarci Sallar Juma'a ba
  • 3 ga watan Mayu bai halarci taron majalisar zartarwa ba karo na uku jere
  • 5 ga watan Mayu ya halarci Sallar Juma'a a Abuja
  • 6 ga watan Mayu ya sake tafiya Birtaniya neman magani
  • 6 ga watan Yuni Aisha Buhari ta ce yana samun sauki sosai