Jarumin shirin James Bond ya rasu

Asalin hoton, Getty Images
Jarumi Sir Roger Moore, wanda yake fitowa a fina-finai da sunan James Bond ya rasu yana da shekara 89, kamar yadda wata sanarwa daga iyalansa ta bayyana.
Marigayin ya fito a finan-finan kamfanin Bond kamar su Live and Let Die da Spy Who Loved Me da kuma The Man with the Golden Gun.
Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa ne ta shafin Twitter, inda suka ce ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya ne gabanin mutuwarsa.
Mista Roger ya mutu ne a Switzerland, kuma za a binne shi ne a garin Monaco na kasar Faransa kamar yadda ya bukata a cikin wasiyya da ya bari. Sai dai ba a bayyana ranar da za a yi jana'izarsa ba tukuna.

Asalin hoton, Getty Images






