Kwastam ta kona daskararrun kaji na miliyan 350

A ranar Litinin ce rundunar hukumar Kwastom mai kula da gabar tekun Najeriya, ta kona daskararrun kaji na kimanin naira miliyan 350.

Hakanan kuma ta mika wata tabar wiwi ta kimanin naira miliyan 350 ga hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar, NDLEA.

Haka kuma hukumar ta kama tsofaffin tayoyin mota da dama.

Ganyen wiwin dai an shigo da shi ne daga kasar Ghana, yayin da aka shigo da kajin kuma daga Brazil.

Shugaban hukumar mai kula da gabar teku a shiyyar Kudu maso Yamma, Yusuf Umar, ya yi wa wakilin BBC Umar Shehu Elleman, karin haske a kan kamen daskararrun kaji da tsoffin tayoyi da kuma ganyen wiwin: