Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari 'ya yi magana' da Osinbajo ta waya
Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce ya yi magana da Shugaba Muhammadu Buhari ta wayar tarho.
Mista Osinbajo, wanda ya shaida wa manema labarai da ke fadar shugaban kasar hakan, ya ce shugaban kasar yana cikin koshin lafiya.
A cewarsa, "Ina son na shaida muku cewa shugaban kasa yana cikin koshin lafiya; mun yi magana da shi da ranar nan, mun yi tattaunawa mai tsawo. Ya nuna sha'awarsa kan yadda muke tantance kasafin kudi da kuma ci gaban da aka samu a kan hakan."
Mukaddashin shugaban kasar ya kara da cewa, "Kuma kamar yadda kuka sani a yau mun yi taro da 'yan kasuwa masu zaman kansu a kan shirin ceto tattalin arziki daga tabarbarewar da ya yi. A kan wannan ma, shugaban kasar ya so jin irin ci gaban da aka samu".
Haka kuma mun gaya masa abubuwan da muka gani, na zanga-zangar da aka yi inda muka shaida masa irin abubuwan da mutane ke cewa game da halin da tattalin arziki ke ciki. Yana cikin kyakkayawan yanayi, sannan ya ji dadin hirar da muka yi.
Da aka tambaye shi kan ko yaushe Shugaba Buhari zai koma Najeriya, sai Farfesa Osinbajo ya ce, "Kamar yadda shugaban ya rubuta wa majalisar dattawa, yana bukatar a gudanar da gwaje-gwaje a kansa kuma da zarar an fitar da sakamakon gwaje-gwajen, likita zai ba shi shawara kan yanayin lafiyarsa. Don haka muna sa ra n zai dawo nan ba da jimawa ba."