Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
NNPC na ci gaba da binciken mai a arewacin Nigeria
A Najeriya, kamfanin man kasar, wato NNPC ya sake komawa yankin Chadi don ci gaba da bincike da nufin gano ainihin adadin mai da iskar gas din da ke karkashin kasa a yankin.
A wata hira da BBC, shugaban kamfanin man Najeriya, Dr Maikanti Baru, ya ce NNPC zai yi amfani da wasu manyan na`urori wajen yin binciken.
Ya kara da cewa idan har abun da aka samu ya kai wani mizani, to kamfanin zai dukufa wajen hakar man.
Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma kamfanin NNPC suka yi hasashen cewa za a iya samun mai a yankin, kuma tun daga wancan lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken man amma ana dakatarwa saboda wasu dalilai, ciki har da zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.