Ƴan sama jannatin da suka kafa tarihi a duniyar wata sun dawo

Asalin hoton, SpaceX
Tawagar Polaris Dawn ta dawo kan doron ƙasa bayan shafe kwana biyar a sararin sama, a wani lamari mai cike da tarihi.
Kumbon da ke ɗauke da tawagar ya sauka a tekun Florida da ƙarfe 07:37 GMT, kuma an yaɗa saukar tasu kai-tsaye a shafin X.
Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka ta ce tafiyar ta yi nasara, kuma za ta share fagen ziyarar buɗe ido da mutane za su riƙa biya ana kai su sararin samaniya.

Asalin hoton, SpaceX

Asalin hoton, SpaceX
Fararen hula huɗu ne suka yi tafiyar wadda hamshaƙin attajiri Jared Isaacman ya ɗauki nauyi, kuma sun kai har zuwa wajen da babu wani ɗan'adam da ya shiga a sararin samaniya, fiye da shekara hamsin da ake zuwa saman.
Scott Poteet, tsohon matuƙin jirgin saman rundunar sojin saman Amurka ne ya tuƙa kumbon, kuma a cikin tawagar abokan tuƙin sa akwai ma'aikatan SpaceX, Sarah Gillis da Anna Menon.
Mr Isaacman da Ms Gillis sun zamo mutane na farko da basu da horo da suka taɓa yin tafiya a sararin samaniya, lamarin da ya ƙunshi amfani da dabaru sosai wajen shige da fice.
Kafin yanzu dai masana da ƙwararru ne kaɗai ke yunƙurin irin wannan tafiya.
Hotunan da aka yaɗa sun nuna yadda su biyun suka fito daga cikin kumbon, sannan suka zagaye shi.

Asalin hoton, SpaceX
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Da yake magana ga cibiyar tattara bayanan tafiyar tasu a Hawthorne da California, yayin tafiyar, Isaacman ya ce “Muna da babban aiki a hannu idan muka koma gida, amma a halin da ake ciki a nan — duniya ta yi kyau".
Tawagar ta yi amfani da sabbin kayan sawa da aka ƙera na musamman waɗanda suke da cikakken tanadin duk buƙatun matafiyan, a lokacin ziyarar tasu.
A cikin kwana biyar da suka yi tafiyar, tawagar ta gudanar da gwaje-gwaje fiye da 40 da suka haɗa da bincike kan amfanin ziyarar sararin samaniya ga kiwon lafiyar mutane da kuma gwajin hanyar sadarwa tsakanin na'urorin tauraron ɗan'adam.
Gillis, wadda ƙwararriya ce a kiɗan goge, ta yi tafiyar da kayan kiɗan ta, kuma ta rera waƙar “Rey’s Theme” from “Star Wars: The Force Awakens,"
An aike da kiɗan nata zuwa duniyar mu, inda aka yi gwajin ingancin sadarwa daga duniyar mutane zuwa sararin samaniya.
An naɗi bidiyon da haɗin gwiwar sashin bincike na asibitin yara na St. Jude wanda Polaris ke ƙoƙarin tara wa ƙudi.
Tawagar ta kasance a cikin kumbon Dragon da aka yi wa laƙabi da Resilience a sararin samaniya na tsawon kwana biyar, tun da suka tashi daga safiyar Talata a cibiyar bincike ta Kennedy da ke Florida.
Wannan tafiya ta kafa tarihin nisan tafiyar da aka yi a sararin samaniya, inda ta kai nisan kilomita 1,400, kuma ita ce tafiya mafi nisa a samaniya tun bayan ta Apollo da aka yi a 1972.
Tafiyar Polaris Dawn ɗaya ce daga cikin irin ta uku da aka tsara yi tsakanin Mr Isaacman da SpaceX.











