Abin da muka sani kan bidiyon wasu mata da ƴanbindiga ke dukansu a daji

Asalin hoton, Others
Gargaɗi: Wannan labarin na ɗauke da abubuwan da za su iya tayar muku da hankali
Bidiyon wasu mata huɗu da ƴanbindiga ke duka a cikin daji na ci gaba da ɗaukar hankalin ƴan arewacin ƙasar musamman a shafukan sada zumunta.
A cikin bidiyon an ga yadda wasu ƴanbindigar da suka sace matan ke ci gaba da azabtar da su a tsakiyar daji.
Ɓullar bidiyon ya janyo zazzafar muhawara daga jama'a tare da kiraye-kiraye ga jami'an tsaro da hukukomi su taimaka wajen kuɓutar da matan.
Ba wannan ne karon farko da ƴanbindiga ke fitar da bidiyon azabtarwar da suke yi wa mutanen da suka sace ba, a wani mataki na tilasta wa ƴan'uwansa biyan kuɗin fansa.
To sai dai nau'in azabar da ƴanbindigar suka yi wa matan a cikin bidiyon ne ya fi ɗaukar hankali da janyo Allah wadai daga bakunan wasu ƴan ƙasar.
Me bidiyon ya ƙunsa?
A cikin bidiyon da aka ɗauka a cikin daji an ga wasu mata huɗu zaune sanye da hijabai.
An ga yadda ƴinbindigar suka fara bugun matan da bulala, kafin daga baya su koma dukansu da bakin bindiga.
Sun riƙa tilasta wa matan cire hijabansu, sannan suka riƙa caka musu bakin bindigar AK-47 a goshinsu.
Sun riƙa caka musu bakin bindigar har sai jini ya fara ƙwarara daga goshinsu zuwa kan idanu da kuncin, sannan su bar su.
Haka suka riƙa yi musu ɗaya bayan ɗaya, kafin daga baya su tara su wuri guda suka kuma tilasta musu yin magana.
An jiyo matan na roƙon yan'uwansu su taimaka su biya wa ƴanbindigar buƙatar da suka nema domin su sake su.
Daga ina aka sace matan?
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an sace matan ne daga jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Jihar Zamfara na daga cikin jihohin Najeriya da ke fama da ayyukan ƴanbindiga da ke satar mutane domin kuɗin fansa.
Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa an sace matan ne mako uku da suka gabata a unguwar Damɓa da ke kusa da Gusau babban birnin jihar.
''Waɗannan matan iyalan mutum biyu ne da aka sace a unguwar Damɓa cikin dare lokacin da ƴanbindigar suka kai hari garin'', a cewar majiyar.
Ko jami'an tsaro sun yi martani?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kawo yanzu dai babu wani martani daga jam'ain tsaron da ake aiki a jihar.
Kuma duk ƙoƙarin da BBC don ji daga gare su haƙarmu ba ta cimma ruwa ba.
Jihar Zamfara na cikin jihohin Najeriya da suka yi ƙaurin-suna wajen ayyukan ƴanbindiga masu satar mutane domin neman kuɗin fansa.
To sai dai jami'an tsaro da gwamnatocin ƙasar a matakai daban-daban na iƙirarin ƙoƙarin magance matsalar, duk da cewa a wasu lokuta gwamnotocin na zargin juna da sakaci.
Ko a watan Satumban 2025 gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi iƙirarin cewa ya san maɓoyar ƴanbindigar da ke addabar jiharsa.
A cikin wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa a lokacin, Gwamna Lawal ya yi iƙirarin cewa zai iya magance matsalar cikin wata biyu in da yana da iko.
''Na san inda ƴanbindigar suke, amma babu yadda zan iya kawar da su tun da ba ni da iko da jami'an tsaro, suna karɓar umarni ne daga sama (Abuja)'', in ji shi.
''Na rantse da Allah, duk inda wani shugaban ɗanbindiga yake a cikin jihar nan, na sani, in ma ya fita daga jihar nakan sani, da wayar hannuna zan iya nuna maka inda suke a yau, amma ba abin da za mu iya yi, tun da abin ya fi ƙarfinmu'', in ji gwamnan.











