Yadda ake yaudarar ƴanmatan Afirka zuwa aikin haɗa makamai a Rasha

Inuwar wata mace da aka haɗa da hoton tutar ƙasashen Rasha, da Sudan ta Kudu, da kuma wasu jirage marasa matuƙa

Asalin hoton, Getty Images / BBC

    • Marubuci, Mayeni Jones
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 6

Tun daga ranarta ta farko a wurin aiki, Adu ta fahimci cewa ta yi babban kuskure.

"An ba mu tufafin aiki ba tare da sanin me za mu yi ba takamaimai. Tun daga ranar farko aka kai mu ma'aikatar haɗa jirage marasa matuƙa. Muna shiga muka ga jiragen bajaja kuma mutane na ta aiki. Sai suka kai mu namu wurin aikin."

'Yar shekara 23 ɗin daga Sudan ta Kudu, Adau ta ce shekarar da ta gabata ne aka yaudare ta zuwa Alabuga Special Economic Zone da ke yankin Tatarstan a Rasha bisa alƙawarin samun aiki.

Ta nemi gurbi a wani shirin da ake kira ‘Alabuga Start’, inda ake ɗaukar mata matasa 'yan shekaru 18 zuwa 22 akasari daga Afirka da yankin nahiyar Kudancin Amurka da Kudu maso Gabashin Asiya. Shirin kan yi wa matasan alƙawarin bayar da horo kan sanin makamar aiki, da girki, da tarbar baƙi.

Amma ana zargin shirin da yaudara wajen ɗaukar aikin inda ake kai matasan wuraren aiki masu haɗari ba tare da albashi mai tsoka ba. Sai dai ya musanta waɗannan zarge-zarge amma ban da maganar kai matasa wurin ƙera jirage marasa matuƙa.

A kwanan nan aka zargi wasu 'yan Afirka ta Kudu da suka dinga tallata shirin da yin safarar ɗan'adam. BBC ta tuntuɓi mutanen da aka zarga amma ba su ce komai ba.

Ƙiyasi ya nuna cewa shirin ya ɗauki fiye da 'yanmata 1,000 daga Afirka domin aiki a kamfanin ƙera makamai na Alabuga. A watan Agusta gwamnatin Afirka ta Kudu ta ƙaddamar da bincike kuma ta gargaɗi 'yan ƙasar da kada su shiga shirin.

Adau ta nemi BBC ta sakaya sunanta kuma kada a bayyana fuskatarta, tana mai cewa ta fara jin labarin shirin ne a shekarar 2023.

Adau ta shiga shirin ne bayan ta ga wani talla da Rasha ta ɗauki nauyi

Asalin hoton, Supplied to the BBC

Bayanan hoto, Adau ta shiga shirin ne bayan ta ga wani talla da Rasha ta ɗauki nauyi

Ta tuntuɓi masu tallata shirin ta dandalin WhatsApp. "Sun ce na cike wani fom da sunana, shekaru, da kuma dalilin da ya sa nake son aiki da Alabuga. Sai kuma aka tambaye ni na zaɓi fanni uku da nake son na yi aiki."

Adau ta ce ta zaɓi aiki a matsayin mai sarrafa injin jan ƙarafuna. Ta ce ta daɗe tana sha'awar zama injiniya.

"Na so na yi aiki a fannin da mata ba su saba yi ba. Abu ne mai wahala ka ga mace a fannin janye ƙarafuna, musamman a ƙasarmu."

Sai da aka shekara kafin a tuntuɓe ta saboda matsalar biza.

Tikitin Adau na zuwa Tartastan

Asalin hoton, Supplied to the BBC

Bayanan hoto, Tikitin jirgin da aka saya wa Adau na zuwa Tartastan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Lokacin da na isa Rasha akwai sanyi sosai, ban ji daɗi ba."

"Na yi mamaki da zuwanmu sashen kamfanin na Alabuga. Abin da na tsammaci gani kenan. Na ga ma'aikatu da yawa, motoci, da kamfanonin harkar noma da yawa."

Adau ta shafe wata uku tana koyon harshen Rashanci kafin fara aiki a watan Yuli. Kuma tun daga nan ne lamari ya ɓaci.

Ta ce ba a nemi shawararsu ba kan ko za su yi aiki a ma'aikatar haɗa jiragen. Sun sanya hannu kan yarjejeniyar rufe baki ta yadda ba za su taɓa yin maganar aikin da suke yi da wani ba, ciki har da danginsu.

"Mun ɗarsa ayoyin tambaya a ranmu. Mun yarda mu yi aiki a fannin hada-hada amma sai ga mu a ma'aikatar haɗa jirage marasa matuƙa."

Alabuga ya musanta yin amfani da yaudara wajen ɗaukar ma'aikata. "Dukkan wuraren aikin da ɗalibanmu za su yi mun lissafa su a shafinmu na intanet," a cewarsa cikin saƙon da ya turo wa BBC.

Ba a yarda ma'aikata su ɗauki hoto a cikin wurin ba, amma BBC ta nuna wa Adau bidiyon da kafar yaɗa labarai ta Rasha RT ta wallafa na wata ma'aikatar Alabuga da ake haɗa jiragen, kuma ta tabbatar mana cewa nan ne wurin da suka yi aiki.

"Maganar gaskiya game da Alabuga Special Economic Zone ita ce wuri ne na ƙera kayan yaƙi," a cewar Spencer Faragasso na cibiyar Institute For Science And International Security.

"Rasha ta bayyana a fili cewa tana ƙera jirgin samfurin Shahed 136 maras matuƙi a wurin cikin bidiyon da suka fitar. Suna alfahari da wurin da kuma abin da suke cimmawa."

Spencer ya ce akasarin matan da suka yi magana da su kan faɗa musu cewa ba su san nan za a kai su domin haɗa makamai ba.

Adau ta ce da ma ta ƙudiri cewa ba za ta iya ci gaba da aiki a wurin ba.

Ta miƙa neman barin aikin amma sai aka fada mata sai ta bayar da sanarwa tsawon mako biyu kafin ta tafi. A lokacin ne kuma ta ce ta yi wa jiragen fenti da wani sinadari da ya ƙona ta.

"Bayan na koma gida, na duba fatata na ga tana ɓarewa. Muna saka kayan kariya, da fararen tufafi, amma sinadarin kan ratsa duk da haka."

Yadda sinadari ya ƙona fatar abokiyar aikin Adau

Asalin hoton, Supplied to the BBC

Bayanan hoto, Yadda sinadari ya ƙona fatar abokiyar aikin Adau

Ba wannan ne kaɗai haɗarin ba. A ranar 2 ga watan Afrilun 2024, mako biyu bayan Adau ta isa Rasha, dakarun Rasha suka kai wa Alabuga Special Economic Zone hari.

"A ranar mun tashi da ƙararrakin ankararwa kan gobara. Tagogin ɗakunan da ke saman benenmu duka sun tarwatse, sai muka firfito waje.

"Daga baya kuma sai na ga mutane na gudu, da na duba sama sai na ga jirgi maras matuƙi. Daga nan ni ma na shiga gudu har na wuce sauran ma."

BBC ta tantance sahihancin wani bidiyo da Adau ta turo mana na harin ranar, kuma shi ne harin da Ukraine ta kai mafi nisa a cikin Rasha a lokacin.

Hotunan da Adau ta ɗauka kenan ranar da Ukraine ta kai wa kamfanin da suke aiki hari

Asalin hoton, Supplied to the BBC

Bayanan hoto, Hotunan da Adau ta ɗauka kenan ranar da Ukraine ta kai wa kamfanin da suke aiki hari

"Jirgin ya hari ɗakin kwanan da ke kusa da namu. Ya lalata ginin gaba ɗaya, mu ma namu ya ɗan samu matsala."

Daga baya da ta gano tana aiki ne a wurin haɗa makamai, sai ta fara tunani game da harin da aka kai musu kuma ta fahimci cewa dalilin da ya sa aka kai musu harin kenan.

"Ukraine na sane cewa 'yanmatan Afirka da suka zo nan domin su yi aiki suna aikin ne a ma'aikatar haɗa makamai, kuma suna zaune ne a wannan ginin. Mun gani a labarai. Lokacin da aka ce Ukraine ta kai wa fararen hula hari, sun musanta cewa: 'A'a, ba gaskiya ba ne. Waɗannan ma'aika ne da ke haɗa jirage marasa matuƙa."

Wasu 'yanmatan sun tafi ba tare da sanar da jagororin shirin ba bayan harin, abin da ya sa suka ƙwace fasfo ɗin wasu ma'aikatan na ɗan lokaci.

"Zargin da ake yi cewa za mu yi aiki a wurin haɗa makamai, mun zaci farfagandar tsanar Rasha ce kawai," in ji ta.

"Ana yawan yaɗa labaran ƙarya kan Rasha domin ɓata musu suna. Mutane da yawa daga Turai da Amurka sun yi aiki a Special Economic Zone amma sun gudu ne bayan fara yaƙin Ukraine da Rasha saboda takunkuman da aka saka wa Rashar. Bayan Rasha ta fara neman 'yan Afirka su yi aiki a wurin, mun zaci kawai tana neman maye gurbinsu ne."

Bayan Adau ta nemi ta koma gida, sai danginta suka aika mata da tikiti, amma ta ce da yawan 'yanmatan ba su iya samun kuɗin komawa gida ba saboda albashin da suke samu bai kai abin da aka yi musu alƙawari ba.

Ya kamata Adau ta dinga samun dala 600 duk wata, amma kashi ɗaya cikin shida na kuɗin take samu.

Alabuga ya faɗa wa BBC cewa suna bayar da albashi ne iyakar yadda mutum ya nuna ƙwazo da kuma kyakkyawar ɗabi'a a wurin aiki.

Mun yi magana da wata macen daban, wadda ta ce ita ta samu alheri a wurin aikin kuma ta musanta zargin da ake yi wa Alabuga.

"Maganar gaskiya, kowane kamfani na da dokoki. Ta yaya za su biya ka cikakken albashi idan ba ka zuwa aiki, ko ba ka yin sa da kyau? Komai na da ƙa'ida kuma babu wanda aka tilasta wa yin aiki a wurin da bai so ba. Akasarin 'yanmatan da suka bar aikin ba su bi ƙa'ida ba ne. Alabuga ba shi riƙe kowa, mutum zai iya barin aikin a duk lokacin da yake so," kamar yadda matar ta shaida wa BBC.

Amma Adau ta ce aiki a wurin haɗa makaman Rasha babban abu ne.

"Abin ba daɗi. Akwai lokacin da na koma ɗakina na yi ta kuka. Na ji ba daɗi saboda ina aikin haɗa abin da ke kashe rayukan al'umma masu yawa."