Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe kuma yaya za a raba jadawalin neman gurbin gasar Kofin Duniya?
Ƙasashen nahiyar Turai za su san takwarorinsu da za su fafata neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da su ranar Juma'a da misalin 11:00 a gogon GMT a birnin Zurich na Switzerland.
Ƙasashen Turai 16 ne za su samu gurbi a gasar wadda aka faɗaɗa zuwa ƙasashe 48 da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Za a iya kallon yadda za a raba jadawalin a shafin internet na BBC Sports kai tsaye har ma da sharhi a kai.
Yaya abin zai kasasnce - da wa masu masaukin baƙi za su fafata?
Ta yaya za a raba jadawalin neman gurbin Kofin Duniyan?
An sauya tsarin yadda ake neman gurrbin nahiyar Turan, an ƙara yawan rukunai - sannan an yi ƙanana sama da na baya.
Za a samar da rukunai 12 da za su yi wasannin neman gurbi. Kununai shida za su kasance da ƙasashe hudu, yayin da sauran shigan za su zama suna da biyar-biyar.
Tawagogin za su fafata da juna gida da wajen kamar yadda aka saba.
Duk tawagar da ta yi ta ɗaya a kowanne rukuni za ta zama ta samu tikitin Kofin Duniyan, yayin da na biyu za su buga wasannin neman cike gurbi.
Za a ɗauki ƙasashe huɗu cikin 16 da za su yi wasan neman gurbi a gasar.
Shu wane a kan gaba?
Ko wanne rukuni zai kasance da tawagar guda daga cikin kowacce tukunya huɗu. Rukunai shidan za su zama suna da tawaga guda daga tukunya ta biyar. Akwai iyaka ta wacce tawaga ce za ta kasance a kowanne rukuni, da kuma wanda za ta fafata da shi, kamar yadda za a gani a jadawalin da ke ƙasar:
Za a fitar da tawagogin bisa tsarin tukwanen da ke da akwai - sai an fara da tawagogin tukunyar farko sannan ta biyu har zuwa ta ƙarshe.
Tukunya 1: Spain, Germany, Portugal, France, Italy, Netherlands, Denmark, Croatia, ENGLAND, Belgium, Switzerland, Austria
Tukunya 2: Ukraine, Sweden, Turkey, WALES, Hungary, Serbia, Poland, Greece, Romania, Slovakia, Czech Republic, Norway
Tukunya 3: SCOTLAND, Slovenia, Republic of Ireland, Albania, North Macedonia, Georgia, Finland, Iceland, NORTHERN IRELAND, Montenegro, Bosnia-Herzegovina, Israel
Tukunya 4: Bulgaria, Luxembourg, Kosovo, Belarus, Armenia, Kazakhstan, Azerbaijan, Estonia, Cyprus, Faroe Islands, Latvia, Lithuania
Tukunya 5: Moldova, Malta, Andorra, Gibraltar, Liechtenstein, San Marino
Su wane ne za su kasance cikin rukunin tawaga huɗu?
Twagogi hudu da suka je wasan suka da ƙarshe a watan Maris za su tafi rukuni ɗaiɗai na neman gurbin gasar Kofin Duniya daga rukunin A zuwa F.
Wannan saboda an buga wasannin ne a watan Yuni, ba kuma a samu damar wasannin share fagen kofin Duniya a lokacin ba.
An dai raba jadawalin ne a gabanin fara wasannin, wadanda suka je wasan kusa da ƙarshen za su zama kamar masu riƙon wuri ne, misali kamar gwarzuwar gasar Faransa za ta samu rukuni sai Croatia itama da kuma sauran ƙungiyoyi biyun ƙarshe.
Shin akwai wani haramci a gasar?
Saboda dalilai irin nasiyasa, Ukraine da Belarus ba za su kasance a rukuni guda ba, kazalika Gibraltar da Spain. Dole sai an raba Kosovo da Serbia da kuma Bosnia-Herzegovina daga rukuni daya.
Yanayin gari ka iya zama wani dalilin shi ma. Saboda yiwuwar sanyi Estonia da kuma wasu ƙasashe biyu ne za su iya zama a rukuni ɗaya da suka haɗa da Faroe Islands, Finland, Iceland, Latvia, Lithuania and Norway.
Ba za a haɗa Iceland da tsibirin Foroes wuri guda ba saboda ana musu kallon ƙasashe biyu da yanayinsu ke da haɗari.
Akwai kuma yanayi na yankunan da ƙasashe suka fito, kamar Kazakhstan da Azerbaijan da kuma Iceland ba za su haɗu da juna ba saboda nisan da ke da shi na tafiya zuwa Turai.
Yaushe ne za a fara wasannin?
Za a yi wasannin ne guda 10 yayin hutun ƙasashe da za a samu sau biyar.
Za a yi hutun ne a tsakanin 21 zuwa 25 ga watan Maris, sai 6 zuwa 10 ga watan Yuni, akwai 4 zuwa 9 ga watan 14 ga watan Oktoba sai kuma 13 zuwa 18 ga watan Nuwambar shekara mai zuwa.
Babu wata tawaga da za ta buga wasanni a duka waɗannan lokutan hutu saboda wasanni takwai kawai aka amince a yi.
Wasu tawagogin za su fara a watan Maris wasu kuma a Yuni, amma tawagogin da za a raba a rukunai huɗu sai a watan Satumba za su fara nasu wasannin.
Wasannin cike gurbi kuma za a yi su ne a tsakanin 26 zuwa 31 ga watan Maris ɗin 2026.
Yaushe za a yi Kofin Duniya?
Za a fara Kofin Duniya a ranar 11 ga watan Yuni a birnin Mexico za a kuma a ranar 19 a watan Yuli a New Jersey.
An faɗaɗa gasar zuwa ƙasashe 48 daga 32, kuma za a kwashe kwana 39 ana gudanar da gasar.
Sabon tsarin zai haɗa da rukini 12 da yake ɗauke da tawagogi huɗu ciki, kuma tawagogi 32 da za su yi saura za su je matakin sili ɗaya kwale.