Wasan ruwa da baje-kolin bajintar soji a cikin hotunan Afirika

    • Marubuci, Lucy Fleming
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙayatattun hoyuna daga sassan Afirika

Wani matashi sanye da riga mai uwan hoda da shuɗin wando , ƙafafunsa babu takalmi ya na watsa ruwa a jikin wata matashiyar wadda ta juya bayanta. Wani yaro kuma yaron na daban kuma ya na watsa mata ruwa a gaban ƙofar shiga wani gida a kudancin Protea da ke Johannesburg a Afirika ta Kudu, ranar 1 ga watan Satumba.

Asalin hoton, Siphiwe Sibeko/Reuters

Bayanan hoto, Ƙananan yara a birnin Johannesburg na Afirika ta Kudu su na wasan watsa ruwa a ranar Litini 1 ga watan Satumba.
Ƙafafu biyu sanye da shuɗin wandon Jeans a ƙarƙashin wata daɗaɗɗiyar mota, a wajen bikin baje kolin tsaffin motoci masu ƙayatarwa a birnin Sasolburg na Afirika ta Kudu a ranar 31 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Kim Ludbrook/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Bikin bajen kolin tsaffin motoci a birnin Sasolburg na Afirika ta Kudu.
Ɗaluban makarantar firamare ta Rutoboko su na zaune cikin aji sanye da kayan makaranta. Suna zaune a kan kujerar katako yayin da ɗaya daga cikin su ya ke rubuta sunansa a bangon littafi. A gabansu akwai allon da ake koya masu karatu da shi. An ɗauki hoton ne a ranar Litini 1 ga watan Satumba, a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo.

Asalin hoton, Marie Jeanne Munyerenkana/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Sabon zangon karatu a makarantar birnin Goma na jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, inda mayaƙan M23 da Rwanda ke goyon baya ke riƙe da madafun iko tun daga atan Janairun bana.
Shanu su na shan ruwa a ƙauyen Bisil na ƙasar Kenya. Wata yarinya sanye da riga mai ruwan hoda ta na ɗibar ruwa daga fanfo. Sauran yara su na tsaye a gefe su na jira ta gama domin su ɗiba nasu. An ɗauki hoton ne a ranar Juma'a 29 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Gerald Anderson/Anadolu/Getty Images

Bayanan hoto, An kai dabobi wajen shan ruwa a ƙauyen Bisil da ke a yankin Kajiado na ƙasar Kenya a ranar Juna'a, yankin da ake fama da fari.
Masu kiwon zuma su na yin hayaƙi a tsaunin Morocco. An ɗauki hoton ne a ranar Juma'a 29 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Abdel Majid Bziouat/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Masu kiwon ƙudan zuma su na yin hayaƙi, yayin da su ke zagayen gonarsu a wani tsauni a ƙasar Morocco.
Jerin gwanon tumaki su na hawa kan tsaunin Aït Attou Moussa da ke yankin Tinghir na ƙasar Morocco. An ɗauki hoton ne a ranar Asabar 30 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Abdel Majid Bziouat/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Wani makiyayi ya na kora tumakansa a kan tsaunin Aït Attou Moussa a ranar Asabar.
Makaɗan sojojin fadar shugaban ƙasar Burkina Faso sanye da kaya masu kalar tutar ƙasarsu, yayin da suke nuna bajinta a dandalin Red Square na birnin Moscow.

Asalin hoton, Evgenia Novozhenina/Reuters

Bayanan hoto, Makaɗan sojojin fadar shugaban ƙasar Burkina Faso sun baje kolin basirarsu a wajen bikin kaɗe-kaɗen soji na Rasha da aka yi a dandalin Red Square na birnin Moscow.
Wani yaro mabiyin ɗarikar katolika riƙe da turaren wuta yana jagorantar sauran yara mabiya addinin kirista a wani tattakin bauta, dukkan su sanye da fararen tufafi a cocin Saint Augustin da ke birnin Conakry na ƙasar Guinea. An ɗauki hoton ne a ranar Lahadi 31 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Patrick Meinhardt/AFP/Getty Images

Bayanan hoto, Wani yaro mabiyin ɗarikar katolika ya jagoranci sauran yara kiristoci a yayin tattakin ibadah a birnin Conakry a ranar Lahadi.
Wani matashin makiyayi a tsaye cikin raƙumansa sanye da rawani da carbi a wuya, a birnin Mogadishu na Somalia, a ranar Talata 2 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Feisal Omar/Reuters

Bayanan hoto, A ranar Talata wani makiyayi tare da raƙumansa a baban birnin Somalia, Mogadishu, a wajen bikin baje kolin raƙuma 1,200 da za a yanka a yayin bikin Maulidin bana.
Ntombizodwa Samane, mahaifiyar Amantle Samane sanye da kallabi mai ruwan ɗorowa da rigar sanyi mai ruwan hoda tana kuka a ƙofar kotun birnin Johannesburg, yayin da ɗiyarta ke riƙe da ita a ranar Litinin 1 ga watan Satumban 2025.

Asalin hoton, Luba Lesolle/Gallo Images/Getty Images

Bayanan hoto, A wata kotun birnin Johannesburg na Afirika ta Kudu, wata uwa da aka yi wa ɗiyarta fyaɗe ta fashe da kuka a ranar Litinin bayan kotu ta yanke wa mutumin da ya yi wa ɗiyarta fyade hukuncin ɗaurin rai da rai.
Masu ƙirƙirar bidiyo a intanet mata guda biyu, ɗaya sanye da farar riga ɗayar kuma sanye da baƙa su na ɗaukar hoto a yayin wasan gasar firimiya ta Najeriya tsakanin Ikorodu City FC da El-Kanemi Warriors a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena, da ke Onikan a jihar Lagos ta Najeriya a ranar Lahadi 31 ga watan Ogustan 2025.

Asalin hoton, Adekunle Ajayi/NurPhoto/Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mata biyu masu ƙirƙirar bidiyo a Intanet da aka gani su na ɗaukar hotuna a ranar Lahadi, a filin wasan ƙwallon ƙafa da ke Lagos, a yayin wasan gasar firimiya ta Najeriya.