Za a ci gaba da Bundesliga ranar Juma'a daga wasan mako na 16

Lokacin karatu: Minti 1

Za a ci gaba da gasar Bundesliga kakar 2023/25 ranar Juma'a, inda za a ɗora daga wasan mako na 16 a babbar gasar tamaula ta Jamus.

Bayern Leverkusen ce mai rike da kofin, wadda za ta je gidan Borrusia Dortmund ranar Juma'a, shi ne wasa ɗayan da za a buga.

Leverkusen tana ta biyun teburi da maki 32 da tazarar huɗu tsakaninta da Bayern Munich ta ɗaya, ita kuwa Dortmund mai maki 25 tana ta shidan teburi.

Sai a ranar Asabar 11 ga watan Janairu za a ci gaba da wasannin mako na 16:

  • Freiburg da Holstein Kiel
  • Heidenheim da Union Berlin
  • Hoffenheida Wolfsburg
  • Mainz 05 da Bochum
  • St. Pauli da Eintracht Frankfurt
  • Borussia M'gladbach da Bayern Munich

Za a kammala wasannin mako na 16 ranar Lahadi 12 ga watan Janairu:

  • RB Leipzig da Werder Bremen
  • Augsburgda Stuttgart k

Kawo yanzu an buga karawa 135 da cin ƙwallo 445, kuma Harry Kane ne kan gaba a yawan zura ƙwallo a raga mai 14 daga Bayern Munich.

Wasan da ƙungiyar da ta ci ƙwallaye da yawa a gida shi ne Frankfurt 7–2 Bochum.

Wasa uku ne da baƙi suka je suka ɗura ƙwallaye da yawa ya haɗa da na Kiel 1–6 Munich da na Bochum 0–5 Munich da kuma na Bremen 0–5 Munich.

Bayern Munich ta lashe karawa biyar a jere a Bundesliga, Leverkusen ta yi wasa 13 a jere ba tare da rashin nasara ba, ita kuwa Bochum ta yi wasa 14 ba tare da nasara ba.

Kakar Bundesliga ta bana, ita ce ta 62, wadda aka fara tun daga 23 ga watan Agustan 2024, wadda ake sa ran kammalawa ranar 17 ga watan Mayun 2025.

An fara hutu daga kammala karawar mako na 13 ranar 22 ga watan Disamba, wadda aka tsara ci gaba da wasannin daga 10 ga watan Janairun 2025.