Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda za mu hana likitoci yin ƙaura zuwa ƙasashen waje – Pate
Gwamnatin Najeriya ta bayyana matakan da take dauka na hana tilasta wa likitocin kasar yin ƙaura zuwa kasashen waje.
Wannan dai wata sabuwar manufa ce ta gwamnatin Bola Ahmed Tinubu don kawo sauyi game da yadda ake tafiyar da al'amurran ma'aikatan kiwon lafiya a duk fadin kasar.
A cewar gwamnatin tana fatan wannan manufa za ta magance manyan matsalolin da ke tilasta wa ma'aikatan kiwon lafiya na Najeriya yin ƙaura zuwa kasashen waje, wani abu da aka jima ana korafi a kai.
Harakar kula da lafiyar al’umma na bukatar ma’aikata ingantattu da kuma wadatarsu a fadin asibitocin Najeriya. Sai dai kuma rashin wadatarsu da ƙarancin kayan aikin lafiya wani babban al’amari ne a Najeriya.
Ministan lafiya Farfesa Muhammad Ali Pate ya shaida wa BBC cewa gwamnatinsu na sane da yadda likitoci da ma ma’aikatan lafiya ke yin ƙaura zuwa ƙasashen waje musamman na turai domin samun albashi mai tsoka kuma sun fito da wani sabon tsari.
Ya ce tsari ne da zai taimaka wajen ƙara yawan likitoci da ma’aikatan lafiya, ba tare da ya hana masu son tafiya kasashen waje zuwa ba. Amma manufar ita ce bayar da dama ga waɗanda suke ƙasashen waje su dawo gida Najeriya don su taimakawa wajen inganta kiwon lafiya.
Daga cikin matakan da gwamnati ta ce ta ɗauka su ne bunƙasa asibitoci musamman manya na koyarwa, tare da inganta kayan aikin kiwon lafiyar.
Ministan ya kuma ce za a ƙara inganta cibiyoyi na kula da masu ciwon kansa a ƙasar.
Ya ce a matakin lafiya na farko an horar da ma’aikatan lafiya sama da dubu takwas a jihohin kasar, sannan za a ci gaba da bin matakai na ƙara yawan ɗaliban kiwon lafiya
Tsarin ya kuma shafi bayar da wani ihisani ga likitocin da suka amince za su yi aiki a karkara
“A wannan tsarin mun ce idan mutum ya yi aiki karkara na shekara biyu zuwa uku, za a ba shi lambar yabo tare da ba shi damar aiki a birni da sauƙaƙa yanayin gudanar da aikinsa tare da ba shi ladar aiki”
"Akwai kuma tanadi na yadda za a bayar da dama ga ma’aikatan lafiya bunƙasa iliminsu domin samun ci gaba tare da ba su cikakken tsaro," in ji shi.
Ya kuma ce akwai tsari na ba ni gishiri na ba ka manda, musamman tsakanin Najeriya da ƙasashen turai da likitocin Najeriya ke kwarara.
“Mun ce ƙasashen da ke karɓar likitocinmu da muka koyar, muna so idan sun ɗauki ƴan Najeriya 100, mu kuma su taimaka muna su horar da 100."
Ministan ya ce ƙarin albashin da shugaban ƙasa ya yi ya shafi yin ƙari ga tsarin albashin ma’aikatan kiwon lafiya
Kuma za a tabbatar da an biya dukkanin kuɗaɗen da ma’aikatan ke bin gwamnati domin tabbatar da gyara tsarin aikinsu.
Yawanci likitocin Najeriya na samun aiki ne ko neman sa a kasashen yankin gabas ta tsakiya da nahiyar Turai inda ake biyan albashi da alawus mai tsoka.
Bincike ya nuna likita guda a Najeriya na duba marasa lafiya 4000 zuwa 5000, maimakon tsarin likita daya da zai duba marasa lafiya 600 karkashin shirin Hukumar Lafiya ta Duniya.
Rashin wadatar likitoci da sauran jami'an fannin lafiya, ya dade yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, tare da karancin kayan aiki, da batun karancin albashi da rashin kyautata walwalar likitoci da ke janyo yajin aiki.