Abin da ya sa likitocin Najeriya suke neman aiki a kasashen waje

Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Najeriya ta ce akan samu likitoci shida cikin goma da ke yunkurin guduwa kasashen ketare domin neman ingantacciyar rayuwa kamar yadda wani bincike da aka gudanar a watan Disambar 2021 ya nuna.

 Kungiyar ta ce ana da likitoci masu neman kwarewa kusan 12,297 tun daga matakin tarayya da jihohi da kananan hukumomin da ke Najeriya baki daya.

Shugaban kungiyar likitocin ta kasa, Dakta Dare Ishaya, ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Dakta Ishaya ya ce ''a halin yanzu na san yawancin abokai da abokan aiki na da suke shirin barin Najeriya”.

Yawancin likitocin na samun aiki ne ko neman sa a kasashen yankin gabas ta tsakiya, da nahiyar Turai inda ake biyan albashi da alawus mai tsoka.

A tattaunawarsa da Shirin BBC Newsday, shugaban kungiyar likitocin Dakta Dare Godiya Ishaya, ya ce sun gano dalilai da dama da ke tilasta wa likitocin kaura daga Najeriya zuwa wasu kasashe.

"Mun gano likitocin na tafiya kasashen da tattalin arzikinsu ya fi na Najeriya, cikin batun nan har da matsalar tsaro da kasarmu ke fama da shi.

Baya ga wannan, akwai rashin kayan aiki a asibitocinmu, sai batun albashi saboda likitocin Najeriya na daukar albashin kasa da dala 1,000, idan ma an yi sa’a'' in ji Dakta Ishaya.

Ya kara da cewa, kasashen da likitocin ke komawa ana biyansu albashin sama da dala 1,000.

Kan batun matsalar satar mutane, ya ce masu garkuwa da mutane sun sace likitoci da jami’an lafiya da yawan gaske, inda ‘yan uwa ke shan wahala wajen hada kudade domin biyan fansa kafin a sake su.

‘’Wata babbar matsalar kuma ita ce, ana yawan far wa jami’an lafiya a asibiti, kuma abin takaicin yawanci 'yan uwan marasa lafiya ne ke yin haka.

Ko dai saboda ba a zo duba dan uwansu akan lokaci ba, ba sa la'akkari da karancin jami'an lafiyar da ake fama da su a kasarmu.''

Wani kwamiti da kungiyarmu ta kafa domin tattara bayanan yawan cin zarafin jami'anmu, mun samu korafin far wa jami'anmu 345, a asibitoci daban-daban na Najeriya.

''Wadannan kadan ne daga cikin matsalolin da likitoci ke fuskanta,'' in ji Dakta Ishaya.

Bincike ya nuna likita guda a Najeriya na duba marasa lafiya 4000 zuwa 5000, maimakon tsarin likita daya, marasa lafiya 600 karkashin shirin Hukumar Lafiya da Duniya.

Rashin wadatar likitoci da sauran jami'an fannin lafiya, ya dade yana ci wa 'yan Najeriya tuwo a kwarya, tare da karancin kayan aiki, da batun karancin albashi da rashin kyautata walwalar likitoci da ke janyo yajin aiki akai-akai.