Ambaliyar Ghana: ‘Ruwa ya cinye gida da gonata'

Asalin hoton, THOMAS NAADI/BBC
Awusife Kagbitor na tafiya cikin sauri domin duba gidanta mai ɗaki uku da ya rushe a unguwar Mepe da ke yankin Volta a Ghana.
Ta ce ta ga ruwa na shiga cikin gidan nata daga wani tafki da ke kusa, kuma cikin minti 10, ruwan ya kai har iya wuya.
Da jin labarin cewa ambaliya ta auka wa gidan mahaifiyarsa, wani ɗanta mai suna Kenneth ya gaggauta zuwa gidan tare da yin ninƙaya a ruwan domin kuɓutar da mahaifiyarsa da kannensa.
Matar mai shekara 56 na daya daga cikin dubban mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a kudu maso gabashin Ghana.
Wata annoba ce da take ƙoƙarin fuskanta. Ta zo musu da ba-zata, ba tare da sun kuɓutar da komai ba, kamar yadda ta shaida min a lokacin da hawaye ke kwaranya daga idanunta.
"Ruwa ya cinye duka gonata da gidana. da tufafi kawai na iya fita daga gidan. Sai da na kwashe shekara 14 ina gina gidan, ba ni da inda zan je, babu wani fili da zan gina," in ji Misis Kagbitor.
An yaɗa labaranta, ita da kusan mutum 26,000 da ambaliyar ruwa ya raba da muhallansu.
An samu ambaliyar ne sakamakon ɓallewar tagwayen madatsun ruwan Akosombo and Kpong da ke kudancin ƙasar.
Me ya haddasa ambaliyar?
Ghana na fuskantar ruwan sama mai ƙarfin gaske cikin watannin baya-bayan nan, lamarin da masana suka ce na zuwa sakamakon sauyin yanayi.
Mamakon ruwan saman na ƙara adadin ruwan da ke madatsun ruwan biyu, kuma jami'an da ke kula da madatsun sun ce sun ɗauki kimanin wata guda suna ƙoƙarin kula da madatsun.

Asalin hoton, Getty Images
Madatsun ruwan biyu suke samar da kashi ɗaya cikin uku n wutar lantarkin ƙasar.
Hukumomi sun ce za su rage yawan ruwan da ke ficewa daga madatsun ruwan biyu, yayin da suke lura da yawan ruwan da ke madatsun biyun.
An gina madatsar ruwa ta Akosombo a shekarun 1960, kuma shugaban ƙasar na farko Mista Kwame Nkurma ne ya gina shi da nufin wadata ƙasar da wutar lantarki domin ha baka masana'antu.
Gina shi ya janyo ambaliya ruwa mai ƙarfi a wasu sassan yankin gabas maso kudancin ƙasar, lamarin daya sa aka sauya wa kusan mutum 80,000 muhallansu.
Haka kuma ginin madatsar ya sa an samar da kogin Volta, Kogi mafi girma da ɗan'adam ya samar a duniya.
Ambaliyar ruwa ta wannan shekara na daga cikin mummunar ambaliya da ta taɓa aukuwa a yankin, wadda ta shafi fiye da garuruwan 100 da ke zaune a kusa da madatsun ruwan.
Yaya girman matsalar?
Hukumar daƙile aukuwar bala'o'i ta ƙasar ta ƙiyasta cewa kimanin gundumomi takwas matsalar ta shafa tun ambaliyar ranar 11 ga watan Oktoba.
Gidaje da dama sun rushe yayin da wasu suka nutse, yayin da hukumomi suka fara auna girman matsalar.
Kusan kashi daya bisa uku na al'ummar Mepe da ke yankin da muka ziyarta na cikin matsanancin hali, sakamakon ambaliyar.
Gidajen ba-haya da maƙabartu da shara duk ruwa y tafi da su, lamarin da ke ƙara fargabar ɓarkewar cutuka.
Wutar lantarki da ruwansha mai tsafta ba sa isa yankunan da lamarin ya faru.

Asalin hoton, THOMAS NAADI/BBC
Wani jami'i a yankin mai suna Ahorsu Amos Borlor , ya ce mazauna wurin sun yi watsi da kiran ɗaukar matakan kariya da ya yi ta yi musu a lokacin da madatsun suka fara nuna alamun ɓallewa.
"Akwai kimanin garuruwan 15 a yankin Voltah, kuma takwas daga cikinsu lamarin ya shafe su matuƙa, ruwa ya cinye gonaki masu yawa, lamarin da ya shafi harkokin tattalin arziki. Ba mu ji daɗin abin da ya faru ba, rayuwarmu na cikin hatsari,," in ji Mista Borlor.
Wani mazaunin garin mai suna Brian Foekpa na cikin takaici kan lamarin, ya ce ambaliyar ta faru ne cikin gaggawa don haka bai samu damar kwashe duk abubuwan da ya mallaka ba, sai iyalansa kawai.
"Mashin ɗin da nake amfani da shi wajen sana'ar Okada na cikin ɗakina da ya rushe, ban samu na tsira da shi ba, don haka wannan abu ya taɓani sosai, bani da abin da zan ci, ruwan ya cinye min gonata. A yanzu da nake magana da kai waɗannan tufafin da ke jikina, su ne kawai abin da ya rage min."

Asalin hoton, THOMAS NAADI/BBC
Rundunar sojin ruwan Ghana na taimaka wa wajen aikin ceto, inda ta ce ta kuɓutar da fiye da mutum 8,000 ya zuwa yanzu.
Mataimakin daraktan hukumar, Seji Saji, ya danganta ambaliyar da mamakon ruwan sama da sauyin yanayi ke haddasawa.
"Ruwan da ke kwararowa zuwa madatsun ruwan ya danganta da ruwan da muke samu daga kogunan Burkina Fasso ," in ji shi.
Ya ƙara da cewa hukumarsu ta kafa sansanonin wucin gadi domin taimaka wa mutanen da ambaliyar ta raba da muhallansu.










