Red Bull ta bai wa Klopp aikin shugaban ƙwallon kafar ƙungiyar

Jurgen Klopp

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Red Bull ta naɗa tsohon kociyan Liverpool, Jurgen Klopp a matakin shugaban ƙwallon kafar ƙungiyar.

Mai shekara 57 ɗan kasar Jamus, zai fara aiki ranar 1 ga watan Janairun 2025.

Kamfanin Red Bull shi ne ya mallaki RB Leipzig a Jamus, mai buga Bundesliga da Red Bull Salzburg ta Australia da New York Red Bull mai buga gasar Amurka ta Major League Soccer da ƙungiyar Red Bull Bragantino ta Brazil.

Haka kuma Red Bull yana da hannun jari a Leeds United mai buga Championship, ya kuma kulla yarjejeniyar sa tallan kamfanin a rigar ƙungiyar a farkon shekarar nan.

Red Bull ya ce Klopp ba zai sa hannu a gudanar da aikin yau da gobe ba, amma zai ke bayar da shawara kan yadda za a samu ci gaba da bunkasa wasannin ƙungiyar da masu horar da ita.

Klopp ya lashe kofi takwas a kaka tara a Liverpool, ciki har da Premier League da Champions League, wanda ya ajiye aikin a karshen kakar da ta wuce.

Ya fara aikin horar da tamaula a Mainz a 2001 daga nan ya koma Borussia Dortmund a 2008, inda ya lashe kofin Bundesliga da kai wa wasan karshe a Champions League a 2013.

Ya ajiye aikin jan ragamar Dortmund a 2015 daga nan ya je ya maye gurbin Brendan Rodgers a Liverpool a Oktoban 2015.

Red Bull tana da hannun jari a wasan ƙwallon gora a kan kankara da tseren motoci da tawaga biyu a tseren Formula 1.