‘Ba ma fargabar zaben gwamna duk da ‘yar takararmu mace ce’

Asalin hoton, OTHER
Yayin da ya rage kasa da mako guda a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majlisun jihohi a Najeriya, jam’iyyar APC a jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar wadda ke da ‘yar takarar gwamna mace daya tilo a kasar, ta ce ba ta jin tsoron karawa da kowace jam’iyya.
Mai magana da yawun gangamin yakin neman zaben 'yar takarar gwamnan, Malam Ahmad Sajo, ya shaida wa BBC cewa a shirye suke tsaf a gudanar da zaben gwamnonin.
Ya ce, "A zaben da ya wuce na shugaban kasa, akwai mutane da dama da suka fadi zabe domin har da gwamnoni ma, sannan akwai wasu jihohin da gwamnoninsu na kan Mulki ma amma jam’iyarsu ta fadi zaben shugaban kasa a jihar, don haka batun kada gwamna mai ci mu bay a bamu tsoro."
Malam Ahmad Sajo, ya ce, "Wai batun cewa zaben mace na da wuya mu mun san cewa duk mutumin da yake da tausayi da tausayawa al’umma, dole kaga al’ummar suna sonsa, don haka ita Aishatu Binani, ba ta da wani abu ma da ta fi mayar da hankali a kansa kamar tausayawa al’umma da take yi.”
'Ya'yan jam'iyyar ta APC dai na wadannan kalamai ne a yayin da jama’a da dama ke ganin yadda karawar za ta kaya tsakanin kallabi da rawuna.
Sanata Aisha Dahiru Binani, dai za ta kara ne da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jam'iyyar PDP, wanda ke neman wa'adi na biyu.
Kuma kamar wasu 'yan takara takwarorinta maza, Sanata Binani ta bi lungu da sakon jihar Adamawa tana yakin neman zabe, a wani yanayi da ba kasafai ake ganin mace na takarar kujera mai girma irin ta gwamna ba, musamman ma a arewacin Najeriya, inda lamuran da suka shafi al'ada da addini ke katse wa mata hanzari.
Aisha Binani, dai ta kasance 'yar majalisar wakilai kana likafa ta ja gaba ta zama 'yar majalisar dattawa da ta wakilci gundumar Adamawa ta tsakiya.
Akwai dai al’ummar jihar da dama da ke nuna goyon bayansu ga takarar Sanata Aishatu Binani, wadanda suke gani ita ce tafi ta cancanta.
A ranar Asabar 18 ga watan Maris ne ake sa ran za a yi zaben gwamnan, kuma 'yan magana kan ce inda ba kasa ake gardamar kokawa.











