Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na iya rasa Rashford, Juventus na son Beto
Juventus ta tuntuɓi Everton kan Beto, amma ƙungiyar ba ta son rabuwa da ɗanwasan gaban na Guinea-Bissau mai shekara, 28, domin yana cikin manyan ƴanwasanta maciya raga. (Talksport)
Juventus na dab da cimma yarjejeniya da Manchester City kan ɗanwasan gaba Justin Oboavwoduo. (Sky Sports Italia - in Italian)
Tottenham da Leeds United da Sunderland na sa ido kan matashin ɗanwasan gaba na Real Madrid da Brazil Endrick, wanda ke taka rawar gani a Lyon a matsayin aro. (Fichajes)
Ga alama Manchester United ba za ta iya hana ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford mai shekaru 28 ci gaba da taka leda a Barcelona ba idan har Barca ta biya fam miliyan 26 ƙarƙashin yarjejeniyar karɓar aronsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Nottingham Forest za ta sauya ra'ayi bayan rashin nasarar samun ɗanwasan tsakiya na Inter Milan da Italiya Davide Frattesi, mai shekara 26. (Sky Sports)
Celtic ta yi watsi da tayin fam miliyan 14 daga Nottingham Forest kan ɗanwasan tsakiya na Belgium Arne Engels. (Mail)
Liverpool na son ɗauko ɗanwasan Inter Milan da Netherlands mai shekara 29 Denzel Dumfries. (Fabrizio Romano)
Chelsea na sa ido kan ɗanwasan baya na Nantes da Faransa mai shekara 18 Tylel Tati. (L'Equipe)
Leicester City da Birmingham City na ciki ƙungiyoyin da ke buga Championship da suka tuntuɓi Newcastle United kan ɗanwasan baya Jamaal Lascelles. (Sky Sports)
Brighton na tattaunawa da Marseille kan dawo da ɗanwasan tsakiya da ta bayar aro Matt O'Riley. (Athletic - subscription)