Shin rage wa Afirka ta Kudu maki zai ba Najeriya damar zuwa World Cup?

Asalin hoton, Getty Images
Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi.
Kwamitin ya gano ƙasar ta yi laifi ne wajen amfani da ɗanwasan da bai kamata ya buga wasan ba, wanda tawagar da fafata da ƙasar Lesotho wato Teboho Mokoena da aka buga a ranar 21 ga watan Maris na shekarar 2025.
FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.
FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace nasarar da Afirka ta Kudu ta samu, sannan ta ba ƙasar Lesotho nasara a wasan.
Haka kuma hukumar ta ci Afirka ta Kudu tarar CHF 10,000, sannan shi ma ɗanwasan, Teboho Mokoena ya samu takardar gargaɗi.
Waɗanda aka ladabtar saboda laifukan dai suna da kwana 10 domin ɗaukaka ƙara a gaban kwamitin ɗaukaka ƙara na kwamitin ladabtarwa na Hukumar FIFA.
A yanzu da aka rage wa Afirka ta Kudu maki uku, me hakan ke nufi ga tawagar Najeriya?
Yadda Rukunin C yake
A ranar 9 ga watan Satumba ne tawagar Super Eagles ta Najeriya ta tashi da kunnen doki a wasan da ta buga da tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.
Bayan wasan ne ƙasar Afirka ta Kudu ta ƙara ɗare-ɗare a saman teburi da maki 17 cikin wasa takwas da ta buga a Rukunin C.
Tawagar Jamhuriyar Benin ke biye mata da maki 14, sai kuma Najeriya da ke mataki na 3 da maki 11.
Sai dai kuma Najeriya ta kasance tana da maki ɗaya ne da na Rwanda da ke mataki na 4, sai kuma ƙasar Lesotho da ke da maki 6 a mataki na 5, sai kuma Zimbabwe ta ƙarshe da maki 4.
Ƙasashe tara ko 10 ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya na 2026, wadda ƙasashe 48 za su fafata kuma ƙasashen Amurka da Mexico da Canada za su karɓi baƙunci.
Wane sauyi aka samu?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙa'idar wasannin neman gurbin, duk tawagar da ta ƙare a mataki na ɗaya daga kowane rukuni guda tara na nahiyar Afirka ce za ta samu gurbi kai-tsaye. Daga baya sai a zaɓo huɗu mafiya ƙoƙari da suka ƙare a mataki na 2, inda za a fitar da ɗaya daga cikinsu sannan ta kara da wata tawagar daga nahiyar.
Yanzu da aka rage wa Afirka ta Kudu maki uku, zai zama tana da maki 14 ke nan, daidai da tawagar ƙasar Benin, ita kuma ƙasar Lesotho ta samu ƙarin maki uku zuwa maki tara maimakon shida a baya kafin a ƙara mata maki uku.
Yanzu wasa biyu ne suka rage wa kowace tawaga, inda Najeriya take buƙatar samun nasara a wasannin guda biyu.
Idan ta samu nasara a wasannin da za ta buga da Lesotho da Benin, zai zama Najeriya da maki 17 ke nan jimilla.
Sai dai kuma hakan zai ta'allaƙa ne da wasannin sauran ƙungiyoyin, domin idan Afirka ta Kudu ko Benin daya daga ciki ta ci wasa ɗaya, ta yi canjaras a wasa ɗaya, za ta koma maki 18. Amma idan ta yi rashin nasara a wasa ɗaya, ta ci ɗaya za ta tsaya da maki 17 ne, daidai ke nan da idan Najeriya ta samu nasara a wasanninta biyu na gaba.
Ita Benin yanzu damarta ta ƙaru, kuma akwai wasa tsakanin Najeriya da Benin, wasan da za a iya kira da raba gardama domin shi ne wasan Najeriya na ƙarshe a rukunin na C.
Ke nan Najeriya ta fi buƙatar samun nasara a wasanninta biyu na gaba, sannan Afirka ta Kudu da Benin su rasa wasanninsu biyu na gaba, inda za ta ƙara da maki 17, su kuma suna 14.
Haka kuma idan Najeriya da Afirka ta Kudu suka ƙarƙare da maki ɗaya, Super Eagles na buƙatar ƙwallaye fiye da Bafana Bafana haka ita ma Benin.
Yanzu haka Afirka ta Kudu na da yawan ƙwallaye +8, yayin da Najeriya ke da +2.










