Yadda aka sace mutum huɗu ƴan gida ɗaya a Abuja

Asalin hoton, Getty Images
A daren ranar Lahadi ne wasu ƴanbindiga suka shiga garin Chikakore da ke yankin Kubwa a ƙaramar hukumar Bwari ta Abuja, inda suka yi awon gaba da mutum huɗu ƴan gida ɗaya da suka haɗa da mai gidan mai suna Adesiyan Akinropo da maiɗakinsa da ɗansu da wani wanda ya kai musu ziyara.
Rahotani daga yankin na cewa bayan ƴanbindigar sun bar gidan, sun haɗa da wani maƙwabcinsu, inda waɗanda aka sace a daren ya kama mutum biyar.
Rahotanni daga yankin na cewa ƴanbindigar sun haura 20 a lokacin da suka faɗa yankin, kuma suna ɗauke ne da muggan makamai.
Sai dai mutanen yankin sun nuna takaicinsu kan yadda ƴansanda ba su kawo musu ɗauki ba sai bayan aukuwar lamarin da kusan awa ɗaya da rabi, lokacin da tuni maharan sun riga sun tsere.
Sai dai rundunar ƴansandan ta Abuja ta ce ba su sami labari faruwar al'amarin da wuri ba ne, wanda hakan ya kawo jinkiri.
Samun labarin garkuwa da iyali ɗaya dungurungum a yankin babban birnin tarayya Abuja ya jefa tsoro a zukatan mutanen yankin da abin ya auku, tare da kira a yi duk mai yiwuwa domin gudun komawa gidan jiya a batun zaman ɗar-ɗar da suka kasance a baya.
Mun ƙaddamar da bincike - Ƴansanda
A nata ɓangaren, Runduar ƴansandan babban birnin tarayya Abuja ta ce tuni ta ƙaddamar da bincike kan harin, sannan ta buƙaci mutanen yankin su kwantar da hankalinsu.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Josephine Adeh ta fita, ta ce, "mun samu kiran kar ta kwana da misalin ƙarfe 1 na dare cewa ƴanbindiga sun shiga garin Chikakore, inda nan take muka tura ƴansanda zuwa yankin."
Ta ce binciken farko-farko ya nuna cewa ƴanbindig guda bakwai ne suka je yankin da shiga irin ta ƴan-sa-kai, "suka yaudara mai gidan ya buɗe musu ƙofa, sai suka yi garkuwa da shi da iyalansa. Sannan wata maƙwabciyarsu da ta yi ƙoƙarin kawo musu ɗauki ta samu rauni," in ji ta.
Ta ƙara da cewa matar tana asibiti tana jinya, sannan ta ƙara da cewa tuni suka ƙaddamar da bincike domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin, tare da kama waɗanda suka yi aika-aikar.
"Yansanda na kira ga mutanen yankin da su kwantar da hankalinsu, sannan su cigaba da sa ido, tare da kai bayanin da zai taimaka wa bincike ƴansanda."
Matsalar tsaro a Abuja
Wannan harin ya ɗaga hankalin mazauna babban birnin tarayya Abuja, musaman yankunan da suka yi fama da matsalar tsaro a baya, inda suke fargabar ko dai ayyukan ƴan bindiga da suke tunanin ya tafi ne zai dawo.
A farkon watan nan ne wasu ƴanbindiga da ake zargi sun gudu daga jihar Katsina suka tayar da wani abun fashewa a wata makarantar Islamiyya da ke ƙauyen Kuchibuyi a ƙaramar hukumar ta Bwari wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum biyu.
Ƙaramar hukumar Bwari wanda ke maƙwabtaka da jihohin Kaduna da Neja ta sha fama da matsalolin tsaro a shekarun baya.
Ɗaya daga cikin garkuwa da mutane da aka yi a yankin da ya ɗaga hankalin shi ne sace matashiya Nabiha da mahaifinta, wanda ya ɗauki hankali matuƙa musamman bayan kashe ƴaruwarta saboda jinkirin kai kuɗin fansa.











