Abubuwan da za su iya yin zagon-ƙasa ga sulhu da ƴanbindiga a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 4

Ana samun ƙaruwar ƙananan hukumomi da al'ummomi a Najeriya da ke yin sulhu da ƴanbindiga domin samun kwanciyar hankali.

Hakan na zuwa ne yayin da ƙasar ta hukumomin ƙasar suka gaza shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankunan ƙasar, musamman arewa maso yammacin ƙasar inda ake fama da matsalar ƴan fashin daji.

Batun yin sulhun ya fi shahara ne a jihar Katsina, inda ƙananan hukumomi da dama ke ci gaba da rungumar wannan tsari duk da cewa wasu jihohin da dama na nuna matuƙar adawa da lamarin.

Matakin ya samar da sauƙi a wasu yankunan, duk da cewa a wasu yankunan an ci gaba da kokawa kan yadda irin waɗannan ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da al'umma.

Sai dai masana sun bayyana cewa wannan zaman lafiyar ba lalle ya ɗore ba domin abubuwan da suka haifar da rikicin ba a magance su ba.

A wata tattaunawa da BBC Hausa, Kabiru Adamu, masani kan harkokin tsaro kuma shugaban kamfanin Beacon Consulting ya bayyana cewa duk da cewa an samu sauƙin kai hare-hare a wasu yankuna, akwai dalilai masu ƙarfi da za su iya rushe duk wani sulhu da ake yi da ƴan bindiga.

"Wannan sulhu da aka cimma da ƴanbindiga abu ne na ɗan lokaci, saboda abubuwan da suka haifar da matsalar suna nan a ƙasa," in ji Adamu.

Ya lissafo dalilan da ka iya hana sulhun da ake yi da 'yanbindiga da al'ummomi ɗorewa, kamar haka:

Rashin magance asalin matsalar

Kabiru Adamu ya ce babban ƙalubalen da ake samu dangane da sulhu tsakanin ƴanbindiga da al'ummomi shi ne cewa har yanzu abubuwan da suke janyo matsalar kai hare-haren nan suna nan a ƙasa, ba a kau da su ba.

Wannan in ji shi yana nufin cewa duk da cewa an cimma sulhu da 'yan bindiga, tushen da ke haifar da hare-haren yana ci gaba da wanzuwa kuma za su iya haifar da yiwuwar sake ɓarkewar tashin hankali a nan gaba.

Masanin ya ce a duk inda ake son samar da zaman lafiya mai ɗorewa, to dole ne sai an gano matsalar da ke haddasa rikicin sannan a yi maganinta kasancewar a wasu lokutan ma, maganin matsala na nufin kawar da matsalolin da suka biyo bayanta ko da kuwa ba a samu zaman sulhu ba.

Rashin karɓe makaman ƴanbindiga

Malam Kabiru Adamu ya ce sani ya ƙara da cewa har yanzu makaman da ƴan bindigar ke amfani da su na hannunsu wanda hakan ya kasance babbar barazana ga zaman lafiya.

"Makaman da waɗannan 'yan bindigan suke kai hare-hare da su suna nan hannunsu, har yanzu ba a anshe su ba. Saboda haka, ko wane irin sulhu aka yi, akwai yuwuwar ya rushe a kowane lokaci, a koma gidan jiya," in ji Adamu.

Wannan, a cewarsa, yana nufin cewa koda sun amince da zaman lafiya yau, suna iya sake dawowa da kai hare-hare gobe da karfinsu.

Abin da ya kamata gwamnati ta yi

Masanin ya bayyana cewa akwai abubuwa masu muhimmanci da gwamnati ya kamata ta yi domin tabbatar da ɗorewar zaman lafiya, musamman a yankunan da ake yawan samun hare-haren 'yan bindiga.

Ga jerin matakan da ya bayar kamar haka;

  • Ɗaukar mataki na dindindin wajen magance matsalar tsaro: Adamu ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta yi amfani da hanyoyi na dindindin wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
  • Amshe makaman 'yan bindiga: Masani ya nuna cewa makaman da ƴn biondigar ke kai mhare-hare da su har yanzu yana hannun su wanda shi ne babban barazana ga zaman lafiya. "Saboda haka, gwamnati ta tabbatar da cewa ta anshe makaman 'yan bindigar," in ji Adamu.
  • Bayar da tsari da zai bayyana wa jama'a manufar gwamnati: Masanin ya kuma ce ya kamata gwamnati ta bayyana wa jama'a yadda ake tafiyar da lamuran tsaro da kuma manufofin da take son cimma. "Gwamnati ta fitar da tsari wanda zai bai wa 'yan ƙasa fahimtar abubuwan da ake ciki, me ake yi, ita gwamnati ne ke goyon bayan sulhu da ƴan bindiga kuma me take son ta cimma," in ji shi.
  • Karfafa tsaro a fadin yankuna: Kabiru Adamu ya kara da cewa ya kamata gwamnati ta karfafa jami'an tsaro a yankunan da abin ya shafa tare da bai wa mutanen da hare-hare ya shafa ɗauki da diyya domin su sami abin dogaro.

Ƙananan hukumomi da aka yi sasanci a Najeriya

Daga cikin ƙananan hukumomin da suka shiga irin wannan yarjejeniyar sulhu da ƴan bindiga akwai;

  • Matazu - Jihar Katsina
  • Jibiya - Jihar Katsina
  • Ɓatsari - Jihar Katsina
  • Safana - Jihar Katsina
  • Kurfi - Jihar Katsina
  • Faskari - Jihar Katsina
  • Ɗanmusa - Jihar Katsina
  • Musawa - Jihar Katsina
  • Ƙankara - Jihar Katsina
  • Birnin Gwari - Jihar Kaduna