Abin da ake nufi da matakin amfani da ƙarfin sojan Ecowas

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Manyan hafsoshin tsaron Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas) na kammala wani taron kwana biyu a Juma'ar nan, inda suke tsara matakin sojin da ƙasashen yankin ke shirin ɗauka a kan sojojin da suka hamɓarar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin dimokraɗiyya a Nijar.

Tana ƙara matsa lamba a kan sojoji masu mulki a Nijar, idan dukkan ƙofofin diflomasiyya suka kasa ɓullewa.

Ga dukkan alamu, sojojin Nijar ya zuwa yanzu, sun kasa fahimtar juna da Ecowas.

Ƙwararrun jami'an diflomasiyya da manyan mutane masu ƙima da malaman addini, kai har da sarakuna, ba su iya kawo ɓangarorin biyu kan teburin tattaunawa ba.

Masharhanta sun yi hasashen cewa manyan hafsoshin tsaron Ecowas da ke taro a Ghana, za su ɓullo da tsare-tsaren da rundunar ko-ta-kwana ta ƙungiyar za ta yi amfani da su wajen tura dakarun mamaya cikin Nijar.

Ecowas dai ta ce za ta yi amfani da kayan aikin da take su don wannan mamaya, ko da yake tana maraba da duk wani taimako daga waje.

Tuni shugabannin ƙungiyar suka ce dakarunsu na ko-ta-kwana su kasance cikin ɗamara. Mun yi nazari a kan abin da hakan yake nufi.

Mene ne amfani da ƙarfin soji?

Amfani da ƙarfin soji na nufin yin amfani da sojoji domin tilasta aiwatar da wani abu da ake so ya faru, a cewar Janar Sani Usman Kuka-Sheka (mai ritaya), wani tsohon jami'in soja kuma masanin harkokin tsaro a Najeriya.

Don haka a nan abin da Ecowas ke nufi, in ji shi, shi ne rundunar ko-ta-kwana ta Ecowas ta je ta fatattaki sojojin da suka ƙwace mulkin Nijar, tare da mayar da Shugaba Bazoum kan kujerar mulki.

"Za su yi amfani da ƙarfin bindiga, amma dai ba magana ce ta lalama ba", in ji Kuka Sheka.

Ya ƙara da cewa sojojin ba za su fito fili su yi bayanin hanyar da za su bi don cimma manufarsu ba, saboda ''shi yaƙi ɗan zamba ne, don haka su kaɗai suka san yadda za su bi wajen aiwatar da wannan tsari''.

Sojojin mamaye ta ƙasa

Masana dai sun ce a cikin zaɓin da Ecowas ke da shi, akwai yiwuwar tura dakarun mamaya ta ƙasa zuwa cikin Nijar.

Ƙungiyar ta yi amfani da irin wannan tsari a baya cikin wasu ƙasashe masu fama da rikici na Afirka ta Yamma. Ba dai zaɓi ne mai sauƙi ba, yana buƙatar ɗumbin dakaru da kayan aiki, kafin rundunar Ecowas ta iya mamaye ɗaukacin Nijar. Ƙasa mai girman murabba'in kilomita 1,267,000, ga kuma makekiyar hamada.

Ƙasashen Senegal da Ivory Coast ne zuwa yanzu suka yi alƙawari tura dakaru zuwa Nijar.

Masu sharhi a fannin tsaro sun ce fayyace bayanai game da babban shirin amfani da ƙarfin soja, na iya ɗaukar tsawon makonni kafin ya kammala, sannan mamaye irin wannan, yana ƙunshe da ɗumbin kasada.

Akwai buƙatar maƙudan kuɗi da jigilar ɗumbin kayan aiki ta ƙasa da ta sama. Sannan kuma yana da hatsarin ta'azzara halin taɓarɓarewar tsaron Nijar da ma ɗaukacin yankin Sahel ke fama da shi.

Yana da kasadar haddasa kashe-kashe da ɓarnata ɗumbin dukiya.

Ƙasashen Ecowas da ma sauran abokan ƙawancensu na duniya, lallai ba za su so hakan ba. Mai yiwuwa ne ma za su yi duk wani abu na ganin sun kaucewa hakan.

Aikin dakarun sojoji na musamman

Idan zaɓin tura dakarun mamaya, ya zama mai wahala, Ecowas na iya amfani da aikin dakaru na musamman. Zaɓi ne da ake iya horas da wasu zaratan dakarun ƙundumbala, inda za su kai farmaki cikin shammata da ɗaukar numfashi a ɗan ƙanƙanin lokaci, su kammala abin da aka umarce su, su fito.

Dakarun ƙundumbalar za su ƙaddamar da samame da yin dirar mikiya a kan birane da wasu muhimman cibiyoyin tsaro da harkokin mulki, su ƙwace su daga ikon dakarun sojojin juyin mulki.

Kafin mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed kan mulki. Daga bisani kuma, sai ƙungiyar ta ƙara aika dakaru cikin ƙasar da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kuma doka da oda.

Akwai Ƙasashen Yamma da dama waɗanda za su iya taimaka wa Ecowas da bayanan sirriin da take buƙata don aiwatar da wannan aikin sojoji na musamman a cikin Nijar

Ikemesit Effiong, wani babban mai bincike a cibiyar tuntuɓa kan ayyukan bayanan sirri ta SBM a Najeriya ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa "Lokacin da dakarun za su yi amfani da shi taƙaitacce ne, kuma tuni akwai ƙwarewar da za a iya aiwatar da hakan a Afirka ta Yamma.

Irin wannan aikin sojoji zai fi zama tabbas," in ji Effiong.

Duk da haka, shi ɗin ma yana da irin tasa kasada.

Kasancewar dakarun ƙasashen waje a wasu cibiyoyi suna gadi cikin tsakiyar babban birnin Niamey na iya harzuƙa tarzoma a birnin da ɗaruruwan mutane suka hau kan tituna don nuna goyon baya ga masu juyin mulki da kuma adawa da katsalandan ɗin ƙasashen waje.

Rundunar Ecomog

A 1990, Ecowas ta ƙaddamar da wani aikin tabbatar da zaman lafiya da ba ta taɓa yin irin sa ba, don kawo ƙarshen wani mummunan yaƙin basasa a Laberiya ta hanyar tura rundunar sojojin ƙasashen Afirka ta Yamma, da ake kira Dakarun Sa-ido kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta na Ƙungiyar Raya Ƙasashen Afirka ta Yamma (Ecomog).

An sake tura dakarun Ecomog a karo na biyu zuwa Laberiya a rikicin da ya shafe tsawon shekara 14 wanda ya kawo ƙarshe a 2003.

Ƙungiyar ta Afirka ta Yamma ta kare matakin shiga tsakanin bisa hujjar cewa rikicin ya haifar da illoli a ƙasashe maƙwabta.

Shiga tsakanin ya yi nasara ta wucin gadi wajen dakatar da zubar da jini da kashe-kashen ƙabilanci kuma tun daga sannan mutane da yawa ke kallon matakin a matsayin wani abin koyi na warware rikici a yanki irin na Afirka ta Yamma.

Sai dai an zargi dakarunta da hannu a jerin take haƙƙoƙin ɗan'adam, a cewar Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Human Rights Watch.

Tasirin amfani da ƙarfin soji

Janar Kuka-Sheka ya ce akwai abubuwa da dama da za su yi tasiri, kan Nijar, kafin ma a fara amfani da ƙarfin sojin.

''Takunkuman da Ecowas ta sanya wa ƙasar da suka haɗar da katse wutar lantarki da rufe kan iyakoki, matakai ne da ke durƙusar da gwamnatin sojin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole manyan hafsoshin tsaron su tsara matakan da za su bi wajen amfani da ƙarfin sojin.

Illar amfani da ƙarfin soji

Masana da dama na ganin cewa amfani da ƙarfin soji da ma tarin matsaloli, waɗanda za su shafi mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Kuka Sheka ya ce idan aka yi amfani da ƙarfin soji ta talakawa ne za su fi kowa shan wahala.

''Su fa masu mulkin nan 'yan tsiraru ne idan aka kwakwanta da al'ummar Nijar, don haka idan aka yi amfani da ƙarfin soji ta hanyar kai hare-hare, to talakawa ne fa za su wahala fiye da kima'', in ji shi.

Wata matsalar kuma da matakin zai haifar ita ce shafar dangantaka tsakanin Nijar da wasu kasashen Ecowas.

''Misali in ka duba ƙasa wadda ta fi kowa ƙarfin faɗa-a-ji a ƙungiyar Ecowas ita ce Najeriya, kuma tana da alaƙa ta ƙu-da-ƙut da Nijar musamman yankin arewacin ƙasar", in ji masanin tsaron.

Ya ƙara da cewa Najeriya na da iyaka da Jamhuriyar Nijar ta ɓangaren jihohinta aƙalla bakwai, al'umominsu, na da alaƙar zumunci ko auratayya tsakaninsu.

"A waɗannan yankunan za ka samu wani mutum matarsa daya na Najeriya, ɗayar kuma na a jamhuriyar Nijar, to ka ga irin waɗannan abubuwa akwai matalolin da za a yi la'akari da su''.

Kuka Sheka ya kuma yi kira da hukumomin Ecowas da sojojin da ke mulkin Nijar da su riƙa lura da waɗanan abubuwa.

"Muna kira ga sojojin Nijar su yi la'akari da lafiya da ci gaban ƙasarsu, ya kamata su saurari wannan ƙungiyar domin ci gaban ƙasarsu", in ji Kuka Sheka.

Shin Ecowas da na sojojin da za su yi aikin?

Kuka Sheka ya ce duk da cewa bai san adadin sojojin da ƙasashen Ecowas ke da su ba, amma dai ya ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi.

"'Kuma idan aka yi la'akari da yadda dakarun kungiyar suka yi yaƙi a ƙasar Saliyo da Laberiya an ga yadda sojojin suka yi tasiri, duk da a wancan lokaci babu fasaha da kayan aiki irin ta yanzu'', in ji masanin taron.

Ya kuma ce batun ba yawan sojoji ba ne, abin da ake la'akari da shi, shi ne irin fasaha da makamai da kayan aiki da sojojin na Ecowas ke da shi.

''Yanzu zamani ya kai kana daga Abuja za ka iya cilla makami zuwa Yamai ko Zindir ko wani gari a Nijar", in ji shi.

Masanin tsaron ya ce duk kuwa da irin wannan fasaha ta zamani, da ake da ita, su ma sojojin na Nijar za su iya samun ɗauki daga wasu ƙasashen, musamman ƙungiyar Wagner ta Rasha", in ji Kuka Sheka.

Ƙalubalen da Ecowas za ta fuskanta

Idan Ecowas ta yanke shawarar tura dakaru zuwa Jamhuriyar Nijar, za ta gamu da gagarumin ƙalubale.

Akwai ma barazana daga ƙasashe maƙwabtan Nijar. Ecowas ta dakatar da sojoji masu mulki a Mali da Burkina Faso, su kuma sun ce duk wani matakin soja da za a ɗauka a kan Nijar, za su ɗauke shi a matsayin wani matsayin wata “shelar yaƙi” a kansu.

Nijar ta fuskar shimfiɗar ƙasa, ita ce ƙasa mafi girma a Afirka ta Yamma, don haka tura dakaru zai kasance wani gagarumin ƙalubale ga ƙungiyar Ecowas.

Tattara rundunar sojojin da za ta aika, na iya zama ƙalubale ga wasu mambobin ƙasashe kamar mafi girma a yankin wato Najeriya, suna fama da ƙalubalen tsaro a cikin gida kuma ba lallai ne su iya bayar da sojojinsu ba.

Akwai kuma batun kuɗi ga duk wani mamayen sojoji musammam ma a lokacin da gwamnatoci suke fama da tsadar rayuwa.

Ana ganin matakin diflomasiyya don kai wa ga zaman lafiya a matsayin hanya mafi dacewa ga dukkan ɓangarorin. Sai dai akwai masu cewa shi kansa zaman lafiyar ba abu ne mai sauƙi ba, kuma don kawo ƙarshen yawan juye-juyen mulki a yankin Sahel, sai Ecowas ta yi da gaske.