Real Madrid ta fara kare kofinta da nasara a Champions League

Luka Modrich

Asalin hoton, SNS

Real Madrid ta fara kare kofinta na Champions League da nasara, bayan da ta je ta doke Celtic 3-0 a wasan farko a cikin rukuni ranar Talata.

Tun farko sun kammala minti 45 ba tare da cin kwallo ba, bayan da suka koma zagaye na biyu ne Real ta ci kwallayen uku.

A minti na 56 Vinicius Junior ya fara cin kwallo sai Luka Modric ya kara na biyu minti hudu tsakani, sannan Eden Hazard ya zura na uku a raga.

Wannan shi ne karo na uku da suka kece raini a tsakaninsu

Champions League Talata 6 ga watan Satumbar 2022

  • Celtic 0 - 3 Real Madrid

European Cup Laraba 19 ga watan Maris 1980

  • Real Madrid 3 - 0 Celtic

European Cup Laraba 5 ga watan Maris 1980

  • Celtic 2 - 0 Real Madrid 

Daya wasan rukunin kuwa RB Leipzig ta yi rashin nasara a gida a hannun Shakhtar Donetsk da ci 4-1. 

Champions League

Asalin hoton, SNS

A wannan rukunin na shida Real Madrid ta lashe Champions League 14 a tarihi, ita kuwa Celtic tana da daya.

'Yan wasan da kociyan Real Madrid, Carlo Ancelotti ya je da su Scotland

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Nacho, Rüdiger, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Lucas V., Tchouameni, D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.

Sakamakaoan wasannin da aka buga ranar Talata:

  • Borussia Dortmund 3 - 0 FC Kobenhavn
  • Dinamo Zagreb 1 - 0 Chelsea
  • Sevilla 0 - 4 Manchester City
  • Paris Saint-Germain 2 - 1 Juventus
  • Celtic Glasgow 0 - 3 Real Madrid
  • Benfica 2-0 Maccabi Haifa
  • Red Bull Salzburg 1 - 1 AC Milan
  • RB Leipzig 1 - 4 Shakhtar Donetsk