Chelsea ta ce Potter zama daram, Amrabat ya watsa wa Liverpool kasa a ido

POTTER

Asalin hoton, OTHER

Chelsea ta ce tana goyon bayan kocinta Graham Potter, kuma tana shirin yin tankade da rairayar yan wasa, matsawar sakamakon da take samu a wasanni bai sauya ba. (Telegraph)

Newcastle ta nuna sha'awar sayen dan wasan tsakiyar Portugal Ruben Neves, wanda watanni 18 suka rage masa a kwantiraginsa da Wolves, in ji jaridar Mail.

Arsenal na da kwarin gwuiwa cewa za ta kammala cinikin fam miliyan 80 na sayen dan wasan Ukraine Mykhailo Mudyryk, don ta samu damar saka shi wasan da za ta yi da Manchester United mako mai zuwa.(Times)

Chelsea ma za ta iya sayen dan wasan gaban Faransa Marcus Thuram kan yuro miliyan 10 kacal, don kwantiraginsa da Borrusia Monchegladbach za ta kare a karshen kaka, a cewar jaridar Caught offside.

Liverpool ta tattauna da wakilan Sofyan Amrabat na Maroko, to amma dan wasan tsakiyar na Fiorentina ya fi son tafiya Atletico Madrid, in ji Mirror.

Chelsea da Tottenham sun kyalla idon kan dan wasan gaban Belgium Leandro Trossard, bayan da ejan dinsa ya fitar da sanarwa cewa dan wasan na son barin Brighton. (Football.London)

Manchester United ta samu tayi daga masu sha'awar sayen kungiyar daga Gabas ta Tsakiya, da Asiya da kuma Amurka.

Hakama ana sa ran hamshakin mai arzikin nan dan Burtaniya, Sir Jim Ratcliffe, zai taya kungiyar. (Telegraph)

Anan kuma Wolves ce ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiyar Brazil Joao Gomez daga kungiyar Flamengo. (Fabrizio Romano)

Sai kuma Manchester United, wadda tace dan wasan tsakiyarta Scott McTominay ba na sayarwa bane yanzu, duk da sha'awar daukar dan Scotland din da kungiyoyin Everton, da Southampton da Leeds, da West Ham, da Leicester suka nuna. (90min)