Ci gaba uku da aka samu a fannin lafiya da ba lallai kun sani ba

Haɗin kai da aka samu tsakanin masana kimiyya wajen samar da rigakafin cutar korona ya nuna yadda binciken likitanci ke canza rayuwar mutane kodayaushe.

Kazalika, binciken da aka yi don magance cutar korona, akwai yiwuwar kun samu labarin penicillin da insulin da kuma rigakafin cutar agana lokacin da kuke makaranta.

Amma akwai ci gaba da bincike waɗanda ba lallai ne mun taɓa jin labarinsu ba, amma suna iya canza rayuwar marasa lafiya.

BBC ta tuntubi masu bincike a fannin lafiya uku kuma aka tambaye su abin da za su gabatar a matsayin binciken da watakila ba a san su ba amma suna da ban mamaki.

Sabon maganin kwayoyin cuta daga hade-haden zamanin da - Dr Freya Harrison, Jami'ar Warwick

Masana kimiyya masu neman sababbin maganin rigakafi na fuskantar matsala.

Magungunan da aka riga aka sani na iya daina aiki a jikin mutum idan kwayoyin cuta suka gina garkuwa daga gare su.

Hakan na nufin sai sun shiga wadansu irin wurare domin nemo sabbin sinadarai da za su iya kashe kwayoyin cuta, wurare kamar ramukan kiyashi da karkashin teku - har ma cikin sinadaran da ke kan hancinmu.

Amma wani wuri mai ban mamaki da ƙwararru suka bi don yin nazari shi ne rubuce-rubuce na zamanin baya, da kuma magungunan da kakanninmu suka yi amfani da su.

Ko da kuwa magabatan Dr Harrison ba su da zurfin ilimin cutukan da tawagarta ke da shi, ana sa ran cewa magungunansu na wancan zamanin na iya kasancewa kunshe da sinadaran da za su iya tasiri a yau.

Dakta Harrison ta bayyana cewa: “Cikin shekara shida da suka gabata, muna aiki a kan wani maganin ciwon ido na ingila na zamanin da.

"An yi shi ne ta hanyar hada tsirrai, da ruwan inabi da kuma kayan cikin shanu, kuma mun ga alamun cewa ya iya yin tasiri a gwaje-gwajen da muka yi a dakin bincike"

Binciken dakin gwaje-gwajen da tawagar ta gudanar ya hada da lura da illar da maganin ke da shi a kan dabbobi da kuma mutanen da ke da adadin sinadarin maras yawa a hannu.

Dakta Harrison ta cigaba da cewa: "Abin mamaki a nan shi ne babu wani sinadari daya da cikin maganin da ke wannan aikin - likitan da ya hada maganin nan ba karamin kokari ya yi ba wurin hada wadannan sinadaran don su zama maganin da ke kashe kwayoyin cuta.

"Yanzu muna aiki don gano ainihin sinadarin da ke wannan aikin, da kuma ganin ko za a iya amfani da shi wajen kashe kwayoyin cutar da ke bijire wa magungunan da muke da su a yanzu."

Ana tsammanin maganin zai iya taimaka wa mutanen da suka ji rauni ko kuma suka kone.

Masu bincike suna ci gaba da bincika litattafan likitanci na tarihi, don ganin hanyoyin da za su iya yin amfani ga marasa lafiya a yau.

Gudu na iya haifar da sababbin sinadarai a cikin kwakwalwa - Dr Daniel Berg, Jami'ar Aberdeen

Likitocin ƙwaƙwalwa sun kiyasta cewa kwakwalwar dan Adam na dauke da kusan kwayoyin halitta biliyan 100, waɗanda ke aikawa da kuma karbar sakonni tskaninsu. Suna kunshe da wani sinadari da ake kira 'Neural stem cell'.

A wani cigaba da aka samu na baya bayan nan, masana kimiyya sun gano cewa bangaren kwakwalwa da ke kula da koyon abubuwa tare da tunawa da su mai suna hippocampus na kunshe da 'neural stem cells' wadanda ke gina sinadarin neuron guda 700 a kullum.

Wadannan nueron din su ne ke tabbatar da halin da muke ciki, suna taimaka mana wurin tunawa da sabbin abubuwa da kuma taimaka mana gane sabbin wurare.

Domin nazarin yadda nueron ke haduwa, masana kimiyya sun yi nazari a gwaje-gwaje game da yadda suke yaduwa a hippocampus din dabbobi.

Wannan ya hada da bari su yi yawo, wanda hakan ke farfado da 'stem cells' din. Hakan ya haifar da kirkirar sabbin 'neurons' wanda zai iya habaka yadda suke iya tuna abubuwa.

Dakta Berg ya ce game da sabon binciken: "Yanzu masana kimiyya na kokarin samo hanyoyin da za su yi amfani da 'neural stem cell' domin yi wa wadanda suka ji rauni a kwakwalwa magani.

"Idan za mu iya tabbatar da cewa wadanda ke cikin kwakwalwar sun maye gurbin wadanda aka rasa, wannan zai inganta rayuwar marasa lafiya da yawa."

Likitoci za su iya yi wa marasa lafiya aiki daga nesa - Farfesa Roger Kirby

Muna iya danganta mutum-mutumi da ke yi wa mutane tiyata da abin da muke gani a fina-finai, amma mai yiwuwa akwai su tun daga karshen karni na 20.

Hukumar NASA da sojojin Amurka ne suka fara gano abin da za su iya yi, sun yi aiki tare a kan wani samfuri a shekarar 1990 wanda zai bai wa likitoci damar yi wa marasa lafiya aiki ko da suna nesa da su.

Shekara 30 bayan haka kuma sai ga mutum-mutumi sama da 80 da ke tiyata a karkashin hukumar lafiya, NHS, suna taimaka wa likitocin yin tiyata kan masu ciwon daji fiye da 15,000 a kowace shekara.

Likitan ne ke sarrafa su kuma amfani da su na sauƙaƙa aikin. Hakan na nufin marasa lafiya ba za su dade suna jinya ba.