Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace ce Nupur Sharma, matar da ta jawo rikici bayan yin ɓatanci ga Annabi a Indiya?
Babbar Kotun Indiya ta ladabtar da tsohuwar kakakin jam'iyya mai mulki bayan wasu furucinta kan Annabi Muhammad ya haifar da ce-ce-ku-ce a ƙasar.
Kotun ta faɗawa Nupur Sharma cewa "harshenta mara linzami ya kunna wutar rikici a ilahirin ƙasar".
Kalamanta a lokacin wata muhawara da aka haska a gidan Talabijin sun haifar da rikici a wasu sassan ƙasar da tunzura ƙasashen Musulmi da dama aike bukatar gargaɗi mai tsauri kan Indiya.
Kotu ta buƙaci ta bayyana gaban Talabijin domin neman gafarar 'yan ƙasar baki ɗaya.
Ms Sharma ta roƙi kotu ta hana bincike-binciken da take fuskanta a sassa daban-daban na ƙasar.
Kotu ta yi watsi da bukatar, tana mai cewa " wannan korafi ne cikin rashin ɗa'a, kuma kotunan ƙasar sun fi karfinta."
Lauyanta ya shaidawa kotu cewa ya nemi afuwa da kuma janye kalamanta.
Amma masu shari'a na cewa "ta makara waje janye kalaman nata, kuma tayi hakan ne bisa sharaɗi, tana cewa idan hakan ya ɓata ran wasu".
Kotun ta ce kasancewa mai magana da yawun jam'iyya, bai ba wa mutum lasisi faɗin din abin da yake so ba domin baƙanta ran mutane.
Ms Sharma ita ce mai magana a madadin jam'iyyar BJP mai mulki lokacin da ta yi waɗannan kalamai.
An dakatar da ita daga jam'iyyar bayan ƙasashen musulmi da dama ciki harda UAE, da Saudiyya da Qatar da Iran sun shigar da korafinsu na adawa a hukumance cikin diflomasiyya.
End of Karin labaran da za ku so karantawa
Batun ya kasance gagarumin barazana ga yunkurin Indiya na inganta huldar diflomasiyarta da ke neman sukurkucewa da wadannan ƙasashe.
Kotun ta kuma fahimci cewa "hakan da ta aikata shi ya kai ga matsalar da aka samu a Udaipur".
Jihar da ke arewacin Rajasthan na cikin yanayi na zama ɗar-ɗar bayan wasu maza biyu Musulmai sun fille kan wani tela Hindu.
Sun naɗi lokacin da suke aikata hakan da ɗaura bidiyon a intanet, suna cewa harin martani ne na nuna goyon-bayan Kanhaiya Lal ga Ms Sharma a shafukan sada zumunta.
Wace ce Nupur Sharma?
Kafin a rabata da aikinta, lauyar mai shekara 37 ta kasance wacce ake yawan tuntuba "kakakin BJP a hukumance" da ake yawaita ganinta ba dare ba rana ana muhawara da ita a tashar Talabijin domin wakilta da kare gwamnatin Firaminista Nerandra Modi.
Ta kasance ɗaliba da ta yi karatun lauya a jami'ar Delhi, Ms Sharma ta soma shiga harkokin siyasa a 2008 lokacin da aka zaɓeta a matsayin shugabar ɗalibai, bayan tsayawa takara ƙarƙashin, Akhil Bharatiya Vidyarthi Parishad (ABVP), wani ɓangare na gangamin ƙungiyar dalibai asalin Hindu ta Rashtriya Swayamsevak Sangh.
Rayuwarta ta siyasa ta samu haɓɓaka sosai a 2011 lokacin da ta koma Indiya bayan kammala digiri na biyu a fannin harkokin kasuwaci ta fuskar shari'a a Jami'ar London School of Economics.
Nuna bajinta da iya kalamai, musamman kokarin da take nunawa wajen gabatar da manufofinta a harshen Hindi da Turancin Ingilishi ya bata damar samun gurbi a kwamitin harkokin yaɗa labarai a zaɓen 'yan majalisar Delhi a 2013.
Shekara biyu bayan haka, lokacin da aka kira sabon zaɓe, ta kasance wanda BJP ta tsayar domin fafatawa da Babban alkalin Delhi, Arvind Kejriwal. Sai dai wannan yanayi da ta jefa kanta ya lalata rayuwarta ta siyasa.