Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jam'iyyu na zargin juna da shirin amfani da ƴan daba a zaɓen gwamnan Kano
A jihar Kano ƴan siyasa sun shiga zargin juna kan yunƙurin amfani da 'ƴan daba don haddasa tashin hankali a lokacin zaɓen gwamna da 'ƴan majalisar dokokin da ke tafe ranar Asabar 11 ga watan Maris.
Haka su ma 'ƴan sanda a jihar suna zargin wasu 'ƴan siyasa da ƙoƙarin ɗauko hayar 'ƴan daba daga waje domin hargitsa al'amura a zaɓen da ke tafe.
Al'amuran siyasar na ɗaukan wannan salo ne da ke jefa fargaba a zukatan mutane yayin da ya rage 'yan kwanaki a yi zaɓukan na gwamnoni da 'yan majalisar dokoki na jihohi a Najeriyar, al'amarin da yake ƙara ta'azzara.
Ɓangarorin 'yan siyasa daban-daban ne ke zargin junansu da yunƙurin amfani da 'ƴan ta-kife domin hargitsa zaɓen na ranar Asabar a Kano.
'Ƴan hamayya da ɓangaren jam'iyya mai mulki na yi wa juna kallon hadarin- kaji.
'Yan takarar gwamna tara ciki har da na jam'iyyar PDP da ADP da ADC sun nuna damuwa tare da zargin cewa wasu abokan fafatawarsu na shirya maƙarƙashiyar haddasa husuma a jihar ta Kano.
Malam Ibrahim Khalil wanda shi ne ɗan takarar gwamna na jam'iyyar ADC ya yi wa BBC ƙarin bayani a madadin sauran.
Ɗan takarar ya ce suna jin ƙishin-ƙishin na irin shirin da ake yi wajen tayar da zaune tsaye a zaɓen gwamnan da za a yi.
Sun ji cewa za a shiga da makamai wajen hargitsa harkar zaɓen inda za a ci zarafin ‘yan takara da masu zaɓe, domin a samu damar yin maguɗi.
Malamin ya ce ba wani kun-ji-kun-ji an san mutanen da suke wannan shiri a don haka ya buƙaci hukumomi da jami’an tsaro da shugabannin al’umma da masu sanya ido na cikin gida da kuma na waje da su san da wannan a gaggauta ɗaukan mataki.
To sai dai ɓangaren jam'iyyar APC mai mulki shi ma ya fito ya yi irin wannan zargi.
Sai dai shi yana nuna yatsa ne ga jam'iyyar NNPP, wadda ya zargi 'ya'yanta da ƙoƙarin haɗa kai domin tayar da zaune-tsaye.
Kwamishinan yaɗa labaran gwamnatin Kano Malam Muhammad Garba ya mayar da zargin kan ‘yan jam’iyyar NNPP inda ya ce sun san irin shiri da kalaman abokan hamayyar tasu a don haka su ne suke da wannan nufi na tayar da hankali.
Kwamishinan ya ce sanin haka ya sa ba za su bayar da damar da za a yi wannan ta’addanci ba domin za su ɗauki mataki na tabbatar da kare doka da oda.
Ya ce magana ce ta dumukuradiyya,’’ idan suna ganin sun fi mu namba to sai a zo a buga a gani idan su suka ci zaɓe, kamar yadda muka faɗa ba mu da zaɓi sai mu ba su idan mu muka ci zaɓe ba yanda za su yi dole su karɓa.
Kwamishinan ya ƙara da cewa idan magana ce ta ƙalubalantar cin zaɓe akwai hanyar da doka ta tanada mutum ya bi amma ba tayar da hankali ba.
Ya ƙara da cewa su ba su da tunanin yin maguɗi a zaɓen saboda suna da yaƙinin cewa dan takararsu na gwamna da sauran ‘yan takararsu suna da nagartar da za su ci zaɓe.
Sai dai ita ma a nata ɓangaren jam'iyyar NNPP ta yi iƙirarin cewa gwamnatin jihar suke zargi da shirya kutungwila ga zaɓen.
Kamar yadda shugabanta na jihar ta Kano, Umar Haruna Doguwa ya shaida wa BBC, inda ya ce ko daga abin da ya faru a zaɓen da ya gabata an gani.
Sai dai shugaban ya ce suna jin daɗin abin da gwamnatin tarayya da shugaban 'yan sanda na ƙasar suke yi kan matakan da ake ɗauka, amma dai ya ce suna ƙara yin kira ne domin hukuma ta sani.
Alhaji Haruna ya musanta zargin da ake yi musu na cewa su ne suke tayar da hankali inda ya miƙa ƙalubale da cewa sai a fito a nuna misalin abin da suka yi kamar yadda su suka kawo misali
Kan zargin shirin maguɗin zaɓe, shugaban ya ce su ai ba su ga dalilin da za a ma yi musu zargin hakan ba domin ai wanda ya ga ba zai ci zaɓe ba shi ne zai yi magudi ya tayar da hankali.
Akasarin 'yan Najeriya dai na ɗaukar zaɓen gwamnoni, a matsayin mai matuƙar tasiri saboda gagarumin ikon da gwamnonin ke da shi a jiharsu da ƙananan hukumomi.
Iko da tasirin da a wani lokacin har sukan dangana da tarayya, inda sukan yi uwa da makarɓiya kan wasu al'amura da suka shafi siyasa da sauran fannonin rayuwar al'ummominsu.