Matar da ke yi wa mata lalle a zamanance

Lokacin karatu: Minti 3

A tsakanin sana'o'in gargajiya da suka shahara a Najeriya, musamman a Arewa, sana'ar lalle ta kasance daga cikin sana'o'in da ke da dadadden tarihi.

Saɓanin wasu sana'o'i da zamani ke yi wa barazana, sana'ar lalle a birnin Zaria ta samu tagomashin fasahar zamani, inda Rabi'atu Sani take amfani da komfuta wajen zana sitika kafin a sanya lalle.

Rabi'atu dai ta fara sana'ar tata ne tun bayan kammala makarantar firamare, inda ta nuna sha'awa ta musamman ga zane-zane.

A tattaunawarta da BBC, ta bayyana yadda ta fara wannan sana'a, inda ta ce:

"Na fara wannan sana'ar tawa ta lalle tun da na gama makarantar firamare, ina son sana'ar zane-zane domin tun a lokacin ma, irin takaddu na zan kama na ringa yin zane-zane, ina zana abubuwan da nake so."

A cewarta, ta fara koyon zanen lalle ne daga wata ƙawarta ta makaranta, inda ta yi gwaji a kan takarda ta kuma fara samun karɓuwa daga mutane.

Yadda Rabi'atu ke yin lallen

Yanzu haka Rabi'atu ta cika shekara 20 tana gudanar da wannan sana'a, tare da yaye yara sama da 100 da suka tafi suna gudanar da nasu sana'o'in a wannan fannin.

Rabi'atu ta ƙara da cewa, "akwai yaran da muke aiki da su da suka haɗa da masu cire zanan da inji ya fitar wanda sun fi 50 da ke zuwa, idan inji ya gama buga zanan lallen da ake mannawa, sai su cicire."

Haka kuma tana da ma'aikata waɗanda ke iya zuwa ko'ina don zana lalle ga kwastomomi.

Rabi'atu ta bayyana cewa amfani da fasahar zamani ya kawo babban canji a sana'arta.

A baya, ana amfani da lallen gargajiya tare da taki wajen saka launin baƙi, amma yanzu ta koma amfani da "mahallabiyya" wanda yake ba da launi mai kyau da ɗorewa.

"Da na fara da Dayis, yanzu zamani ya zo, da lallen gargajiya nake amfani, mun dawo da amfani da zamanin ƴan da kenan, abun da kawai ya ƙaru a lallen gargajiyarmu shi ne 'mahallabiyya' wanda ke saka zanen lallen ya yi baƙi."

Ma'aikata da inganta rayuwar matasa

Rabi'atu ta bayyana cewa duk da cewa wasu suna ganin lallenta na da tsada, ta jaddada cewa inganci da kyau ne ke jan hankalin kwastomomi wanda har yake ga mutane suna yaba wa sana'arta.

Yanzu haka ta ce suna da injina fiye da 20 da ke samar da zanen lalle daban-daban cikin sauri, inda aikin da da ake yi a sa'o'i biyu yanzu ana kammala shi cikin minti talatin.

Rabi'atu ta ce babban burinta shi ne ganin yaran da ta yaye suna ci gaba da samun nasara a wannan sana'a, har ma suna koyar da wasu, wanda hakan ke ƙara taimaka wa tattalin arzikin iyalansu da al'umma baki ɗaya.

A kullum, Rabi'atu ta ce kamfaninta na zana wa mutum fiye da 30 lalle musamman ma a lokutan biki inda ake yi wa mutum kusan 100 lalle a rana.

Ta ce: "kamar lokacin sallah haka, har kati muke bai wa mutane wanda yake ka wa wajen 300 a rana ko fiye da haka ma, idan kuma biki ne, ana wa mutum kusan 100 lalle a rana."

Rabi'atu Sani ta nuna cewa duk da cewa sana'ar lalle tana buƙatar dabara da jajircewa, tare da taimakon Allah da amfani da zamani, ta samu ci gaba da nasara mai girma da ma'ana a wannan fanni inda take ba da dama ga yara da matasa su samu aikin yi, su samu sana'a mai ɗorewa, sannan kuma su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin iyalansu da al'umma baki ɗaya.

Labari Rabi'atu Sani ya nuna mana yadda sana'o'in gargajiya ke iya zama hanya ta samun ci gaba a rayuwa idan aka haɗa su da dabaru da kuma amfani da fasahar zamani.