Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda riga-kafin maleriya zai rage kisan da cutar ke yi wa yara
- Marubuci, James Gallagher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health and science correspondent
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba da shawarar yin amfani da alluran riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro mai arha wanda za a iya samar da shi cikin sauki ga mutane da yawa
Jami'ar Oxford ce ta samar da alluran kuma shi ne maganin zazzabin cizon sauro na biyu da aka amince da shi.
Zazzabin cizon sauro na kashe yawancin yara kanana da jarirai, kuma ya kasance daya daga cikin manyan bala'o'in da ke addabar bil'adama.
An riga an kammala yarjejeniyar samar da fiye da alluran riga-kafin miliyan 100 a duk shekara.
An dauki fiye da karni guda ana gudanar da bnciken kimiyya don samar da ingantattun alluran riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro.
Cutar ta samo asali ne daga wadansu kwayoyin halitta, wanda ke yaduwa ta hanyar cizon sauro. Ta fi kwayoyin cuta muni yayin da take boyewa daga tsarin garkuwar jiki ta hanyar canzawa koyaushe cikin jikin dan adam.
Wannan yana hana garjuwan jiki yaki da cutar bayan kamuwa da ita kuma hake ke haddasa wahalar samar da maganin rigakafin cutar.
Kusan shekaru biyu kenan tun ranar da aka fara yin allurar riga-kafin farko - da ake kira RTS,S da kamfanin GSK ya samar tare da goyon bayan hukumar WHO.
Alluran riga-kafi biyu masu yanayi da juna
Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, darekta-janar na WHO, ya ce wannan lokaci ne na "matukar farin ciki".
“A da ina sa ran ganin ranar da za mu sami ingantattun alluran riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro, yanzu muna da guda biyu,” in ji shi.
Hukumar ta WHO ta ce tasirin alluran rigakafin guda biyu "na yanayi da juna" kuma babu wata shaida cewa daya ya fi daya inganci.
Duk da haka, babban shine yiwuwar kera allurar rigakafin Jami'ar Oxford - wanda ake kira R21 - da yawa.
Babban mai kera alluran rigakafi a duniya - Cibiyar Serum Institute ta India - ta riga ta shirya samar da allurai sama da miliyan 100 a shekara kuma yana shirin habaka har zuwa allurai miliyan 200 a shekara.
A halin da ake ciki yanzu akwai allurai miliyan 18 na RTS,S.
Hukumar ta WHO ta ce sabon rigakafin R21 zai zama "mahimmin karin kayan aiki". Farashin kowanne allura a tashi kan $2-$4 kuma kowanne mutum daya na bukatar allurai hudu. Wannan shi ne kusan rabin farashin alluran RTS,S.
Magungunan guda biyu suna amfani da fasaha iri daya kuma suna yaki ne da bangaren daya na rayuwar cutar. Duk da haka, alluran rigakafin na baya bayan nan ya fi saukinn hadawa saboda yana amfani da sinadarin adjuvant mai sauki (wani sinadari da ke kunshe cikin alluran da ke bunkasa aikin garkuwan jiki).
A shekarar 2021, an sami kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro miliyan 247 sannan mutane 619,000 suka mutu, yawancinsu yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar. A Afirka ne a ke samun fiye da kashi 95% na ciwon zazzabin cizon sauro.
An gudanar da gwajin amfani da alluran R21 a garin Bagamoyo da ke Tanzania. Duk da cewa ya kasance a lokacin tsananin cutar ta Corona, iyaye mata kamar Mwazani Seif sun yi rajista duk da adawar da ta fuskanta a kauyenta. Ta kawo 'yarta 'yar shekara uku, wanda ita ce 'yar ta ta shida don karban allurar.
''Na rasa yaron dan uwa na . Mun birne shi. Shekarunsa hudu e kacal a lokacin d ya mutu sakamakon cutar Malaria. In ji ta. ''Shi ya sa da na ji cewa ana gwajin alluran rigakafin malaria, na ce ina son a yi da ni. Zai taiamakwa yara dayawa, ba nawa kadai ba''.
Yiwuwar ceto rayuka
Dr Matshidiso Moeti, darektan hukumar WHO a Afirka, ya ce: ''Allurar rigakafi ta biyu na da yiwuwar maye babban gibin bukatu da a ke fuskanta.
"Samar da alluran dayawa da kuma fitar da su a ko'ina, alluran rigakafin biyu na iya taimakawa wajen inganta rigakafi kan cutar malaria, da dakile yaduwar cutar da kuma ceto rayukan dubban daruruwan matasa."
Bayanan da aka buga ta yanar gizo, amma wanda ba a bi ta hanyar da aka saba bi na yin bitar kimiyya ba, sun nuna cewa allurar R21 na da tasirin kashi 75% wajen rigakafin cutar a wuraren da zazzabin cizon sauro ke barkewa lokaci zuwa lokaci.
Tawagar kwararrun masu ba da shawara kan dabarun hukumar WHO ta ce adadin ya yi daidai da allurar rigakafin farko (RTS,S) a yakunan da cutar ke afkuwa lokaci zuwa lokaci.
Tasirin allurar rigakafin ya ragu a wuraren da cutar ke yaduwa a ko da yaushe a shekara.
Farfesa Sir Adrian Hill, darektan Cibiyar Jenner da ke Oxford inda aka kirkiro da R21, ya ce: “Ana iya tura allurar cikin sauki, da araha, kuma a shirye ake don rarrabawa a wuraren da ake da matukar bukata, tare da yiwuwar ceton dubunnan rayuka a kowanne shekara."
Gareth Jenkins, daga kungiyar Malaria No More UK, ya ce: "Gaskiyar magana ita ce, samar da tallafi kan zazzabin cizon sauro a duniya bai kai kusa da yadda ake bukata ba kuma mace-macen da ake samu kowanne daga zazzabin cizon sauro ya karu a lokacin barkewar cutar Corona kuma har yanzu ba su sauko ba, don haka bai kamata mu yi kasa a gwiwa ba yayin da ake bullo da sabbin kayayyakin aiki."